Wani Gwamna ya dawo daga yawon duniya, ya sanya dokar ta baci a jaharsa

Wani Gwamna ya dawo daga yawon duniya, ya sanya dokar ta baci a jaharsa

Gwamnan jahar Benuwe, Samuel Ortom ya katse tafiyar da yayi zuwa kasashen waje da yaje hutawa sakamakon matsalar tsaro data dabaibaye jaharsa, wanda hakan yasa ya dawo gida Najeriya, kuma tuni ya kaddamar da dokar ta baci a jahar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu ne gwamnan ya kaddamar da dokar hana shige da fice a garin Katsina Ala sakamakon wani hari da wasu miyagu suka kaddamar a ranar Lahadia a garin.

KU KARANTA: Zargin Buhari na barci akan aiki: fadar shugaban kasa ta mayar ma Fasto da martani

Wannan hari da miyagun yan bindiga suka kaddamar a kauyukan Katsina Ala da suka hada da Ngibo da Tse-Aye yayi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha daya, sa’annan suka yi garkuwa da mutane biyar.

Haka zalika yan bindigan sun yi awon gaba da shanu 28 mallakin wani babban lauya mai suna Barista Agwaza Atedze, sa’annan sun banka ma gidaje da dama wuta, wanda hakan yayi ya sabbaba jama’an Katsina Ala tserewa daga garin.

Mukaddashin gwamnan jahar, Benson Abounu yace dokar ta fara aiki ne daga ranar Litinin, kuma na tsawon awanni 24 ne, inda yace hakan ya zama dole don kyautata tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a.

Sai dai a jawabinsa, kwamandan rundunar Soji ta Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Adeyemi Yekini ya bayyana cewa wannan rikici ya auku ne tsakanin kabilun Shitile da na Ikyurav, dukkaninsu mazauna garin Katsina Ala, amma ya bada tabbacin Sojojinsa zasu shawo kan lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel