Mutum 2 sun mutu, 10 sun jikkata a hatsarin mota da ya afku a hanyar titin Lagas-Ibadan

Mutum 2 sun mutu, 10 sun jikkata a hatsarin mota da ya afku a hanyar titin Lagas-Ibadan

An tabbatar da mutuwar mutane biyu yayinda wasu 10 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku da wata bus kirar Mazda a yankin Danliti Ayetoro kan babbar titin Lagas –Ibadan.

Mista Babatunde Akinbiyi, kakakin hukumar kula da cunkoson ababen hawa, ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abeokuta a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu.

Akinbiyi yayi bayanin cewa lamarin ya afku neda misalin karfe 11:00 na safe, cewa tsananin gudu ba bias ka’ida bane ya yi sanadiyar afkuwar hatsariun.

Ya kuma bayyana cewa motar kasuwan mai lamba DDA 729 XA, bayan ya kwace daga hannun direba, sai ya daki kwalbati sannan ya ta dungure, inda ya kara da cewa direban motan da kwandastan motan ne suka mutu.

Mutum 2 sun mutu, 10 sun jikkata a hatsarin mota da ya afku a hanyar titin Lagas-Ibadan

Mutum 2 sun mutu, 10 sun jikkata a hatsarin mota da ya afku a hanyar titin Lagas-Ibadan
Source: Depositphotos

“Hatsarin ya afku ne sanadiyar gudu da yawa wanda yayi sanadiyar kwacewar motar. Mata hudu da maza takwas ne suka kasance a matsarin amma direba da kwandasta ne suka mutu,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Harin Kajuru: Rundunar yan sanda ta bayyana sunan mutum na biyu da aka kashe a harin

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta kone kafatanin tsangayar ilimi da wani sashe na dakin kwanan dalibai maza kurmus a jami'ar kimiyya da fasaha da ke Aliero, a jihar Kebbi.

Ana kyautata zaton cewar gobarar ta tashi ne sakamakon haduwar wutar lantarki a bangaren tsangayar ilimi na jami'ar.

Gobarar ta kone kafanin ginin tsangayar ilimi, wanda ya hada da ofisoshin malamai da dakunan dalibai na daukan darasi, da kuma wani bangare na dakin kwanan dalibai, kafin daga bisani a samu nasarar kashe ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel