Gwamna Ayade ya nemi Kwamishinoninsa su tanadi takardun ajiye aiki

Gwamna Ayade ya nemi Kwamishinoninsa su tanadi takardun ajiye aiki

Mai girma gwamnan jihar Kuros-Riba, Ben Ayade, ya bada umarni ga daukacin Kwamishinonin jihar da su kawo masa rahotannin da su ka rubuta game da aikin da su kayi a ofis a shekaru kusan 4.

Ben Ayade ya ba Kwamishinonin na sa wa’adi zuwa Ranar Juma’ar nan, 26 ga Watan Afrilun 2019 da su mika masa dukkanin takardun barin ofis. Ayade ya samu zarcewa ne a kan mulki a zaben bana a karkashin jam’iyyar PDP.

Gwamnan yayi wannan sanarwa ne ta bakin babban Sakatarensa na yada labarai wanda kuma shi ne ke taimaka masa wajen harkokin yada labarai, Mista Christian Ita. Ita yace gwamnan yana so a gama wannan aiki kafin Juma’a.

KU KARANTA: Kashi 95% din mu ba mu da karfin kara albashi – Gwamnan Ebonyi

Gwamna Ayade ya nemi Kwamishinoninsa su tanadi takardun ajiye aiki

Kwamishinonin Kuros Riba za su fara shirin nade kafar wandon su, su bar Gwamnati
Source: Facebook

Gwamnan ya kuma fara shirin rage yawan ma’aikatan jiharsa, wanda hakan yana nufin za a zaftare wasu Kwamishinoni. Sai dai abin mamakin shi ne, gwamnan yana cikin wadanda su ka fi kowa yawan Hadimai da Mukarrabai.

Ayade yana da Kwamishinoni, da Masu ba shi shawara da Mataimaka da Hadimai fiye da 10, 000 a halin yanzu. A wa’adin sa na biyu, Ayade ya nuna cewa zai rage yawan tarin Mukarraban na sa domin yayi wa jama’an jihar aiki da kyau.

Mun ji cewa Gwamna Ayade ya fadawa Kwamishinonin su fara shirin barin-gado inda ya nuna cewa wasu Kwamishinonin sa za su fara shirin nade kafar wandon su, su ba sa iska a cikin Gwamnati

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel