Zargin Buhari na barci akan aiki: fadar shugaban kasa ta mayar ma Fasto da martani

Zargin Buhari na barci akan aiki: fadar shugaban kasa ta mayar ma Fasto da martani

Fadar shugaban kasa ta bayyana zargin da wani Fasto Stephen Mamza yayi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na sharer barci a bakin a matsayinsa na babban kwamandan askarawan Najeriya, a matsayin tsantsagwaran rashin adalci.

Kaakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu, inda yace abin kunya ne ace Fasto kamar Mamza yana tsoma baki cikin lamurran siyasa da bashi da kwarewa akai.

KU KARANTA: Aikin ashsha! Yadda Uwargida ta halaka Maigidanta da wuka a jahar Kebbi

Zargin Buhari na barci akan aiki: fadar shugaban kasa ta mayar ma Fasto da martani

Buhari
Source: UGC

“A wani mataki na yin kaca kaca da tsarin kaurace ma siyasa, shugaban mabiya darikar katolika a jahar Yola, Rabaran fada Stephen Mamza ya gabatar da huduba a coci yana caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari, har yana bayyanashi a matsayin babban kwamanda bai barci akan aiki.

“Wannan ba adalci bane, akwai abubuwa da dama da aka samu sauyinsu a cikin shekaru uku zuwa hudu da suka gabata a garin Yola, kai har ma a cocin katolikan kanta, wanda da ba don zuwan Buhari da abubuwa basu canza ba, kila ma da sun ta’azzara, hakan ba zai taba yiwuwa ba da barci Buhari yake yi.

“Sanin kowa ne Mamza na cikin kwamitin zaman lafiya na API, dake aikin kula da yan gudun hijira sama da dubu dari hudu a yankin Arewacin Adamawa da jahar Borno, a shekarar 2015, haka nan sune wadanda suka kwantar da hankula tsakanin Musulmai da Kiristoci.

“A farfajiyar cocin St. Theresa kawai, cocin Mamza, akwai yan gudun hijira 1,500, wanda yawancinsu mata ne da kananan yara, wadanda cocin take basu abinci, kuma mun yaba da wannan aikin alheri nasa.” Inji shi.

Sai dai Garba ya tuna ma Mamza cewa tun bayan hawan gwamnatin Buhari data karya lagon Boko Haram, sama da yan gudun hijira 400,000 sun koma gidajensu a Adamawa da Borno, haka zalika Sojoji sun kwato garuruwan Michika, Madagali da Mubi, wanda Boko Haram ta mamaye.

Haka zalika a cewar Garba, gwamnati tare da hadin gwiwar kugiyoyi masu zaman kansu suna sake gina hanyoyi, asibitoci, gadoji, wutar lantarki, makarantu, kasuwanni, coci coci da masallatan da Boko Haram ta lalata a yankunan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel