Shugabancin majalisa: Dalilin da yasa nake goyon bayan Lawan da Gbajabiamila – Tinubu

Shugabancin majalisa: Dalilin da yasa nake goyon bayan Lawan da Gbajabiamila – Tinubu

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa baki daya, Bola Tinubu ya bayyana cewa bashi da wata manufa daban na goyon bayan Sanata Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila wajen ganin sun zama Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai.

Tinubu ya yi watsi da rade-radin da ake yin a cewa yana share wa kansa hanyar zama dan takarar Shugaban kasa na APC a zaben 2023.

Jigon na APC ya ce ya na goyon bayan mutanen biyu ne domin mara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, ta yadda zai samu nasarar gudanar da mulki a zangon sa na biyu.

Ya ce an yi kuskure a 2015, inda aka yi sakaci har Sanata Saraki da Hon. Dogara suka zama shugabannin majalisa, inda suka shafe shekaru hudu su na rike kasafin kudi tare da kawo tsaiko kan muhimman ayyukan raya kasa da Shugaba Buhari ya sha alwashin samar wa ’yan Najeriya.

Shugabancin majalisa: Dalilin da yasa nake goyon bayan Lawan da Gbajabiamila – Tinubu

Shugabancin majalisa: Dalilin da yasa nake goyon bayan Lawan da Gbajabiamila – Tinubu
Source: Depositphotos

Tinubu ya ce kwata-kwata wannan ba gaskiya ba ne a ce wai ya na azarbabin neman takarar shugabancin kasar nan.

A cikin wata takarda da ofishin Tinubu ya fitar, wadda Jami’in Yada Labarai Tunde Rahman ya sa wa hannu, Saraki ya ce irin yadda akidar siyasar ta ta sa gaba ta zama shaida a gare shi cewa shi ba mutum ne mai kwadayin mulki ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Wadanda suka yi garkuwa da masu ciki 2 da wasu 3 sun nemi a basu N20m

Ya ce tun bayan da ya gama wa’adinsa na gwamnan jihar Lagas daga 1999 zuwa 2003, bai sake neman wani mukamin siyasa ba.

Ya ce ya mayar da hankali ne wajen ganin ya kafa jam’iyyar da za ta bangaje jam’iyyar PDP daga mulki. Wannan nasara ce ya ce ya samu a 2015, bayan ya hada guiwa da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ma mutum ne mai kishin ci gaban kasar nan kamar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel