Yanzu Yanzu: Wadanda suka yi garkuwa da masu ciki 2 da wasu 3 sun nemi a basu N20m

Yanzu Yanzu: Wadanda suka yi garkuwa da masu ciki 2 da wasu 3 sun nemi a basu N20m

Yan bindigan da suka yi garkuwa da mata masu ciki biyu da wasu mutane uku a garin aria da ke jihar Kaduna sun nemi a biya su naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwan sun kira daya daga cikin iyalan wadanda abun ya cika dasu domin isar da bukatarsu.

Anyi garkuwa da mutanen su biyar daga gidajensu a ranar Lahadi da misalin karfe 2:00 na tsakar dare.

Masu garkuwan, wadanda suka kai mamaya yankin dauke da muggan makamai, sun zabi matan ne sannan suka tafi dasu zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Yanzu Yanzu: Wadanda suka yi garkuwa da masu ciki 2 da wasu 3 sun nemi a basu N20m

Yanzu Yanzu: Wadanda suka yi garkuwa da masu ciki 2 da wasu 3 sun nemi a basu N20m
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa harda wata malamar makaranta mai ciki cikin wadanda aka sace.

“Tabbass, sun kira sannan sun bukaci naira miliyan 20 a matsayin kudin fansar dukkaninsu su biyar din. Ana kan tattaunawa da masu garkuwan domin ceto su.

“Muna addu’a Allah ya kawo dauki saboda daya daga cikinsu malamar makaranta ce mai ciki. Allah yak are su damu baki daya, Ameen,” inji ahlin daya daga cikin wadanda abun ya shafa bayan ya nemi a sakaya sunansa.

An tattaro cewa lamarin yayi sanadiyar gudanar da gagarumin zanga-zanga a garin inda matasa suka kare babbar titin Nnamdi Azikiwe a ranar Lahadi.

Har sai dai hukumomin tsaro suka shiga lamarin sannan aka tarwatsa dandazon jama’an domin su bar hanyar.

A wani lamai makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa rundunar yan sandan jihar Kaduna a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu ta bayyana sunan mutum na biyu da masu garkuwa da mutane suka kashe tare da yar kasa Birtaniya a Kajuru da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun dakile zanga-zangan a saki Dasuki a Sokoto

An bayyana sunansa a matsayin ‎Mathew Danjuma Oguche wanda ke aiki da wata kungiya mai zaman kanta na kasa da kasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwan sun sanya naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa akan mutum uku da aka sace a lokacin harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel