Karin albashi: Zai yi wahala Gwamnoni su rika biyan N30000 – Umahi

Karin albashi: Zai yi wahala Gwamnoni su rika biyan N30000 – Umahi

- David Umahi na jihar Ebonyi yace karin albashi fa zai yi wahala a Najeriya

- Gwamnan ya bayyana cewa kusan kashi 95% na Gwamnoni ba za su iya ba

- Gwamnati ta maida N30, 000 ya zama mafi karancin albashi yanzu a Kasar

Gwamna David Umahi ya fito ya bayyana cewa zai yi wahala gwamnonin jihohi su iya dabbaka sabon albashin da gwamnatin Najeriya ta kayyade. Gwamnan yace mafi yawan gwamnoni ba za su iya biyan wannan albashi ba.

Mai girma gwamnan na na jihar Ebonyi ya bayyana cewa kashi 95% na gwamnonin kasar, ba su da ikon biyan Ma’aikatansu sabon albashin da aka kawo. Yanzu mafi karancin albashin Ma’aikaci ya zama N30, 000 a Najeriya.

Dave Umahi a Ranar 17 ga Watan Afrilu, yake cewa idan har ana so gwamnoni su rika biyan wadannan makudan albashi, ya zama dole a sake duba tsarin kason kudin da ake yi tsakanin jihohin Najeriya da kuma gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Jerin Jihohin da za su iya biyan sabon karin albashi

Karin albashi: Zai yi wahala Gwamnoni su rika biyan N30000 – Umahi
Umahi yace Gwamnoni ba za su iya karawa Ma’aikata albashi ba
Source: Depositphotos

Gwamnan yayi wannan jawabi ne wajen wani zama inda ya kaddamar da kwamitin da zai duba batun albashi da alawus din ma’aikatan kasar. Umahi yake cewa akwai bukatar jihohi su rika samun kudin da ya fi abin da su ke samu.

A tsarin da ake kai a yanzu, gwamnatin tarayya na karbe kashi 52% na abin da Najeriya ta samu yayin da jihohi ke raba sauran kason. Umahi yace dole a sake duba wannan tsari, muddin ana so a rika biyan ma’aikatan jihohi N30, 000.

Mista Umahi yace babu abin da zai sa ya karar da kudin jiharsa wajen biyan albashi kurum. Umahi yake cewa a halin yanzu dole sai ya hada da cin bashi sannan zai iya biyan ma'aikata albashi, yayin da yake da sauran aiki a gabansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel