Yan sanda sun dakile zanga-zangan a saki Dasuki a Sokoto

Yan sanda sun dakile zanga-zangan a saki Dasuki a Sokoto

- Hukumar yan sanda ta dakile wani shirin zaga-zanga da ake yi domin neman a saki tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki a Sokoto

- Jagoran shirin yace hukumar ta bayar da hujja na tsaro a matsayin dalilin hana masu izinin aiwatar da hakan

- A cewarta hankali bai gama kwantawa ba tun bayan sake zabe da aka gudanar

Rundunar yan sanda ta dakile wani shirin zaga-zanga da ake yi domin neman a saki tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) a jihar Sokoto.

Jagoran zanga-zangan, Abulsamad Dogondaji, ya fada ma majiyarmu ta Daily Trust cewa an shirya gudanar da zanga-zangan ne a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu kafin yan sanda su soke ta.

A cewarsa, hukumar yan sandan ta ki basu izinin gudanar da zanga-zangan akan dalili na halin da tsaro ke ciki a jihar.

Yan sanda sun dakile zanga-zangan a saki Dasuki a Sokoto
Yan sanda sun dakile zanga-zangan a saki Dasuki a Sokoto
Source: Depositphotos

“Kwamishinan yan sandan ya fada mana cewa har yanzu akwai tashin hankali biyo bayan sake zabe da aka gudanar a jiha sannan cewa ba za su bayar da dammar da za a karya kowani doka da zaman lafiya da oda ba a jihar.

“Amma dai muna shirin zanga-zangan lumana ne wannan ne yasa muka rubuta wasika muna neman izininsu da kariyarsu,” ya jadadda.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya samar da ayyuka miliyan 12- Ministan labarai

A lokacin da aka kira, kakakin rundunar, DSP Muhammad Sadiq, ya bayyana cewa hana masu izini da akayi saboda lamarin tsaro ne a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel