Shugaba Buhari ya samar da ayyuka miliyan 12- Ministan labarai

Shugaba Buhari ya samar da ayyuka miliyan 12- Ministan labarai

- Gwamnatin shugaba Buhari ta yi ikirarin cewa ta samar da bagiren ayyukan yi sama da miliyan 12 a shekaru hudu da tayi kan mulki

- Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai

- Yace sun samar da sabbin ayukkan ne a fannin noman shinkafa da kuma shirin ciyar da dalibai a makaranta wanda ya samar da aikin yi ga masu dafa abinci, N-Power da dai sauransu

Gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi ikirarin cewa ta samar da bagiren ayyukan yi sama da miliyan 12 a shekaru hudun farko da tayi tana mulki.

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da majiyarmu ta BBC, inda ya jadadda cewa sabbin ayyukan da suka samar sun hada da wadanda aka kirkira kai-tsaye da kuma wadanda suka tallafa aka samar.

Shugaba Buhari ya samar da ayyuka miliyan 12- Ministan labarai

Shugaba Buhari ya samar da ayyuka miliyan 12- Ministan labarai
Source: Depositphotos

Mohammed ya kara da cewa sun samar da sabbin ayukkan ne a fannin noman shinkafa da kuma shirin ciyar da dalibai a makaranta wanda ya samar da aikin yi ga masu dafa abinci.

KU KARANTA KUMA: Mu na nan daram a kan zargin da mu ke yiwa rundunar sojin sama - Sarakunan jihar Zamfara

Sannan ya kara da cewa N-Power ya samar wa matasa dubu biyar aikin yi da kuma shirin bayar da tallafi ga kananan 'yan kasuwa na tireda moni wanda ya samar da sabbin ayyukan yi ga mutane sama da miliyan biyu.

Matsalar rashin ayyukan yi na cikin matsalolin da ke addabar 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel