Shugaban Majalisa Saraki ya kalubalanci Tinubu ya kare zargin da ye jefa masa

Shugaban Majalisa Saraki ya kalubalanci Tinubu ya kare zargin da ye jefa masa

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya nemi babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya kawo hujjoji na zargin da yake yi masa na yin cushe a cikin kasafin kudin Najeriya.

Tsohon gwamnan na Legas, Bola Tinubu, ya zargi Bukola Saraki da kuma Takwaransa Yakubu Dogara na majalisar wakilai, da yin kare-kare da rage-rage da kuma cusa wasu ayyukan da su ka ga dama a kasafin kudin Najeriya a duk shekara.

Yanzu dai Bukola Saraki ya maidawa Tinubu martani ta bakin wani Hadiminsa watau Yusuph Olaniyonu. Shugaban majalisar yace akwai ganganci da rashin sanin abin da ya dace da kuma son-kai a cikin kalaman na Bola Tinubu.

KU KARANTA:

Shugaban Majalisa Saraki ya kalubalanci Tinubu ya kare zargin da ye jefa masa

Tinubu bai san yadda Majalisa ta ke aiki ba – Saraki
Source: UGC

Tsohon gwamnan na Kwara ya nemi Bola Tinubu ya janye kalaman na sa da yake zargin sa da kuma Yakubu Dogara da rashin tausayi da yin abin da zai taimakesu kadai a majalisa ba tare da la’akari da sauran mutanen Najeriya ba.

Jawabin na cewa Saraki ya saba da caccakar Tinubu duk kusan bayan watanni 3, Sanatan yake cewa idan aka duba tun daga 2010, za a ga cewa an saba kamalla aikin kasafin kudi a Najeriya ne tsakanin Watan Maris zuwa Mayu.

Shugaban Sanatocin ta bakin Olaniyonu yake cewa ya kamata Tinubu ya san cewa dole sai hukumomin gwamnatin tarayya sun zo gaban majalisa sun kare kasafinsu, kafin ‘yan majalisa su amince da kundin kasafin wannan shekarar.

KU KARANTA:

A jawabin na sa na Ranar Litinin, 22 ga Watan Afrilu, ya kuma caccaki Tinubu a game da tsoma baki cikin batun majalisa inda yace jigon na APC yayi ta kokarin yadda zai yi na ganin bayan shugabannun majalisar a gwamnatin nan.

Hadimin shugaban majalisar ya bayyana cewa gazawar da Tinubu yayi na kakabawa majalisa wanda za su jagorance ta a 2015 ne ya sa ya zama bai da wani aiki sai sukar Bukola Saraki domin ya hana mutanen sa samun kujera.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel