Hukumar Kwastam ta samu N311B a cikin farkon shekarar 2019

Hukumar Kwastam ta samu N311B a cikin farkon shekarar 2019

Hukumar Kwastam mai yaki da fasa kauri a Najeriya, ta samu kudi har Naira Biliyan 311 daga farkon shekarar nan zuwa yanzu. A cikin watanni 3 rak ne hukumar ta tara wannan makudan kudi.

Kamar yadda labari ya zo mana, a cikin shekarar 2019 nan, jami’an Kwastam sun tara Biliyan 311.2. Joseph Attah, wanda shi ne ke magana a madadin hukumar Kwastam na kasa ya bayyana wannan a cikin Garin Abuja.

Rahoton ya nuna cewa a Watan Junairun bana, Kwastam ta samu Biliyan 116.5, yayin da hukumar ta samu Biliyan 84.9 a Watan Fubrairu. A cikin watan jiya na Afrilu kuwa, hukumar ta iya tattaro kudi har Naira Biliyan 109.8.

KU KARANTA: Arewacin Najeriya na cikin babbar matsala - Sarki Sanusi II

Dama can gwamnatin tarayya ta nemi hukumar ta Kwastam ta tara akalla Naira Biliyan 887 a bana. Shugaban gidan Kwastam din na Najeriya, Kanal Hameed Ali mai ritaya ya sha alwashin sake cin ma wannan buri a 2019.

Joseph Attah yace hukumar Kwastam ta na samun kaso mafi tsoka na kudin ta ne daga yankin Apapa na Legas, sannan kuma tashar Tincan da ke cikin jihar ta Legas a dalilin shigo da manyan kaya da ake yi ta wannan shiyyar.

Idan ba ku manta ba a bara ne hukumar ta Kwastam ta samu kudi har Naira Tiriliyan 1.2. A wani bangare kuma wata kungiya ta NACCIMA a Najeriya ta nemi gwamnatin shugaba Buhari ta dafawa ‘yan kasuwan da ke cikin gida.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel