Mu na nan daram a kan zargin da mu ke yiwa rundunar sojin sama - Sarakunan jihar Zamfara

Mu na nan daram a kan zargin da mu ke yiwa rundunar sojin sama - Sarakunan jihar Zamfara

Kungiyar sarakunan jihar Zamfara tayi watsi da rahotannin da ke bayyana cewar ta nemi afuwar rundunar sojin saman Najeriya (NAF) a kan zargin cewar dakarun NAF sun yi ruwan wuta a kan farar hula.

Da yake maga da manema labarai a ranar Litinin, shugaban kungiyar sarakunan jihar Zamfara kuma sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, ya bayyana rahoton da cewar bashi da tushe balle makama.

A cewar sa: "na karbi bakuncin tawagar shugabannin rundunar sojin sama karkashin jagorancin Air Vice Marshall Idi Lubo, sun zo ne domin jajanta wa jama'a a kan kuskuren kashe fararen hula da suka yi yayin luguden wuta.

"A cikin jawabin da na gabatar, babu inda na nemi afuwar rundunar NAF a kan fitar da sunayen farar hula da suka yi kuskuren kashe wa yayin luguden wuta a wasu wurare da suke zargin sansanin 'yan ta'adda ne, kawai na yi amfani da lafazi mai taushi ne kamar yadda ya ke a al'adar fada na girmama manyan bakin ta."

Mu na nan daram a kan zargin da mu ke yiwa rundunar sojin sama - Sarakunan jihar Zamfara

Shugaban rundunar 'yan sanda da Sarakunan jihar Zamfara
Source: Twitter

Ya ce babu yadda za ai sarki mai girma kamar shi ya fadi maganar da ba zai iya kare kan sa ba.

"Ban yi magana ba sai da muka gama tattara hujjoji yayin zaman majalisar sarakuna kuma mun tabbatar da cewar an kashe fararen hula, idan har zan fadi magana daga baya na dawo na canja zance, to ban cancanta na cigaba da zama a matsayin sarki ba," a cewar sa

DUBA WANNAN: Gobarar tsakar dare ta yiwa tsangayar ilimi da dakin kwanan dalibai kurmus a jami'ar Kebbi

Alhaji Attahiru ya kara da cewa NAF ta dauki alhakin kisan fararen hular, har ma ta bayyana cewar hakan ya faru ne bisa kuskure, saboda aikinsu shine kare lafiya da dukiyoyin 'yan kasa na gari.

"Jagoran tawagar NAF ya mika sakon ta'aziyya, amadadin shugaban rundunar sojin sama, ga jama'ar jihar Zamfara.

"A matsayin mu na sarakuna, ba niyyar mu ba ce mu bata sunan rundunar sojin sama, mun bayyana sunayen wadanda aka kashe ne a matsayin martani ga kalaman ministan tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan Ali (mai ritaya), wanda ba tare da wani dalili ba ya zargi sarakunan Zamfara da hada baki da 'yan bindigar jihar," a cewar sarkin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel