Aikin ashsha! Yadda Uwargida ta halaka Maigidanta da wuka a jahar Kebbi

Aikin ashsha! Yadda Uwargida ta halaka Maigidanta da wuka a jahar Kebbi

Wata Uwargida mai shekaru 25 da haihuwa, Hafsat Sani ta burma ma Maigidanta, Muhammad Garba wuka a mararsa, sakamakon wata yar cacar baki data kaure a tsakaninsu, wanda hakan yayi sanadiyyar shekawarsa lahira.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Litinin, 25 ga watan Maris a gidansu dake kauyen Tudinfari, cikin karamar hukumar Suru ta jahar Kebbi, inda a wannan rana ne ma’auratan suka samu sabani, har cacar baki ya shiga tsakaninsu, daga nan Hafsa ta rarumi wuka ta caka ma Garba.

KU KARANTA: Alheri gadon barci: Attajiri ya fara rabon kayan Sallah ga gajiyayyu da talakawa a Sakkwato

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kwamishinan Yansandan jahar Kebbi, Garba Muhammad Danjuma ya bayyana cewa tuni sun kama Hafsat, kuma suna gudanar da binciken kwakwaf akanta kafin su turata gaban kuliya manta sabo.

A wani labarin kuma, kwamishinan Yansandan ya bayyana nasarar da suka samu na kama wasu miyagu da suka kashe wata mata Balkisu Zayyanu da diyarta yar shekara uku, Hadiza Zayyanu a unguwar Dolekaina, cikin karamar hukumar Kamba ta jahar Kebbi.

“A ranar 22 ga watan Maris na 2019 wasu mutane biyu, Jamilu Musa da Alhaji Alu suka afka dakin uwargida Balkisu inda suka yi amfani da igiya, turmi da tabarya suka kasheta, sa’annan suka kulle diyarta a cikin akwati, inda anan ta mutu.

“Sai dai da fari, zakara ya basu sa’a, inda suka tsere daga gidan mamatan dauke da wayoyinta guda biyu, amma daga bisani bincike yayi bincike har muka kama wadanda suka sayi wayar, Harisu Umar da Bello, inda suka kaimu ga Jamilu da Alu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel