Mun kashe kaifin kungiyar Boko Haram - Gwamnatin Najeriya

Mun kashe kaifin kungiyar Boko Haram - Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta jaddada matsayinta a kan cewar ta karya fika-fikan kungiyar Boko Haram sannan ta kashe kaifin aiyukan ta'addanci da mayakan kungiyar ke yi.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ne ya fadi hakan yayin da ya bayyana a wani shirin gidan talabijin din TVC da ake nuna wa da safe, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Ministan ya ce duk wanda ke son sanin ko wannan gwamnatin tayi kokari wajen yaki da aiyukan ta'addanci, musamman wajen murkushe kungiyar Boko Haram, ya tuna yadda lamura suke a bayan kafin zuwan gwamnatin APC a shekarar 2015.

"Kafin zuwan gwamnatin mu a shekarar 2015, mayakan kungiyar Boko Haram na kai hari duk birnin da suka ga dama, ciki har da Abuja. Sai sun zabi inda suke son su kai hari. Ba su bar hatta ofishin majalisar dinkin duniya da hedikwatar rundunar 'yan sanda ba.

Mun kashe kaifin kungiyar Boko Haram - Gwamnatin Najeriya

Lai Mohammed da wasu ministoci a wurin taron kwamitin zartar wa na gwamnatin tarayya.
Source: Depositphotos

"A tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014, kungiyar Boko Haram na da karfi a jihohi a kalla 10, inda suke kai hari a duk lokacin da suka ga dama. Sun kwace iko a kananan hukumomi 17 na jihar Borno, hudu a jihar Adamawa da biyu a jihar Yobe.

DUBA WANNAN: Gobarar tsakar dare ta yiwa tsangayar ilimi da dakin kwanan dalibai kurmus a jami'ar Kebbi

"Mutane da yawa sun mance cewar kafin shekarar 2015, harkoki sun tsaya cak a yankin arewa maso kudun; bankuna sun rufe, an rufe makarantu, masana'antu sun tsayar da aiki, an rufe hanyoyi, kamfanonin sadar wa sun fara janye jiki, hatta kungiyar kwallon kafa ta jihar Borno sai Bauchi ta koma da taka leda," a cewar Mohammed.

Sannan ya kara da cewar akwai kalubalen tsaro a ko ina cikin fadin duniya, ya ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da aiki da ragowar kasashen duniya wajen ganin an murkushe duk wata kungiya da aiyukan ta'addanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel