Gobarar tsakar dare ta yiwa tsangayar ilimi da dakin kwanan dalibai kurmus a jami'ar Kebbi

Gobarar tsakar dare ta yiwa tsangayar ilimi da dakin kwanan dalibai kurmus a jami'ar Kebbi

Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta kone kafatanin tsangayar ilimi da wani sashe na dakin kwanan dalibai maza kurmus a jami'ar kimiyya da fasaha da ke Aliero, a jihar Kebbi.

Ana kyautata zaton cewar gobarar ta tashi ne sakamakon haduwar wutar lantarki a bangaren tsangayar ilimi na jami'ar.

Gobarar ta kone kafanin ginin tsangayar ilimi, wanda ya hada da ofisoshin malamai da dakunan dalibai na daukan darasi, da kuma wani bangare na dakin kwanan dalibai, kafin daga bisani a samu nasarar kashe ta.

Wani jigo a jami'ar da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce jami'ar ta kafa kwamiti domin ya gudanar da bincike a kan musababbin tashin gobarar.

Gobarar tsakar dare ta yiwa tsangayar ilimi da dakin kwanan dalibai kurmus a jami'ar Kebbi
Gobarar tsakar dare ta yiwa tsangayar ilimi da dakin kwanan dalibai kurmus a jami'ar Kebbi
Source: Twitter

Gobarar tsakar dare ta yiwa tsangayar ilimi da dakin kwanan dalibai kurmus a jami'ar Kebbi
Wani sashe na tsangayar ilimi da wutar ta yiwa kurmus a jami'ar Kebbi
Source: Twitter

Ya ce abin takaice ne cewar wannan shine karo na biyu da gobara ta taba tafka barna a jami'ar.

DUBA WANNAN: Tsagwaron kishi: Wani magidanci, Danjuma ya kashe matar sa saboda ta ce za ta sake aure idan ya mutu

"Duk lokacin da gobata ta tashi haka take tafka barna kafin a kashe ta saboda babu sashen kashe gobara a cikin jami'ar," a cewar sa.

Da ya ziyarci jami'ar ranar Litinin domin ganewa idonsa, gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya dauki alkawarin cewar gwamnati za ta gyara dukkan wuraren da wutar gobarar ta lalata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel