Jami’an Yansanda sun kama mayakan Boko Haram guda 4 (Hoto)

Jami’an Yansanda sun kama mayakan Boko Haram guda 4 (Hoto)

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun samu nasarar cafke wasu gungun mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a jahar Edo, cikin yankin kudu masu kudancin Najeriya, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rundunar Yansandan jahar Edo ta bayyana sunayen yan ta’addan kamar haka Salihu Uzovehe (23), Hadi Musa Gambari (23), Tijani Garuba (24) da Mohammed Abdulkadri (44).

KU KARANTA: Basu ji ba, basu gani ba: Dansanda sun tattake mutane 9 da mota, sun jikkata 32 a Gombe

Jami’an Yansanda sun kama mayakan Boko Haram guda 4 (Hoto)

Jami’an Yansanda sun kama mayakan Boko Haram guda 4
Source: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa mayakan na Boko Haram suna liken asiri a jahar Edo, tare da aikin fashi da makami da kuma satar mutane, tare da garkuwa dasu don neman kudin fansa a tsakanin jahar Edo da jahar Kogi.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Chidi Nwabuzor ya bayyana cewa aikin hadaka tsakanin rundunar Yansanda da hukumar tsaron farin kaya na DSS ne yayi sanadiyyar kama mayakan na Boko Haram.

“Daga sahihan bayanai da muka samu daga hukumar DSS, tare da hadakan ofishin babban sufetan Yansandan Najeriya, ya nuna yan ta’addan na kokarin kaddamar da hari a sansanonin Yansanda, daga nan ne kwamishinan Yansandan DanMallam Mohammed ya bada umarnin kamasu.

“Da wannan umarni ne yasa a ranar 19 ga watan Mayu muka kaddamar da wani samame a yankin Auchi, inda muka kamasu duka, daga cikin abubuwan da muka kama sun hada da Mota kirar Toyota Valet, bindigar Pump Action, kananan bindigu 2, alburusai, kayan Yansanda, rigar fuska da layu.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yayi kira ga jama’a dasu ankara da tare da lura da masu shige da fice a yankinsu, sa’annan ya nemi su kawo karar duk wanda basu gane take takensa ba ga jami’an Yansanda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel