Basu ji ba, basu gani ba: Dansanda ya tattake mutane 9 da mota, ya jikkata 32 a Gombe

Basu ji ba, basu gani ba: Dansanda ya tattake mutane 9 da mota, ya jikkata 32 a Gombe

Wasu jami’an tsaro da suka hada da jami’in Dansanda guda, da jami’in Civil defense sun tafka aika aika a jahar Gombe, inda suka kashe wasu kananan yara guda 9 yayin da suke tattakin bikin Easter na Yesu Almasihu a daren Lahadi, 21 ga watan Afrilu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya auku ne da misalin karfe 11:30 na daren Lahadin a daidai mahadar hanya ta Alheri dake kan babbar hanyar Biu cikin birnin Gombe, inda jami’an tsaron suka tare ayarin mabiya addinin Kirista dake gudanar da tattakin Ista.

KU KARANTA: Watsi da hadisin Annabi ya janyo ma wani makwabci shiga tsaka mai wuya

Wani shaidan gani da ido, Isaac Kwadang ya bayyana cewa jami’an tsaron suna cikin motar gida ne a lokacin da suke iske ayarin kiristocin, inda suka yi cacar baki da wasu matasan dake cikin ayarin har suka basu hanyar wucewa.

“Amma da suka yi gaba, sai suka dawo baya, suka kashe fitilar motarsu, suka afka cikin ayarin masu tattakin, nan take suka kashe kananan yara guda takwas, tare da jikkata mutane 31, wannan ya harzuka sauran masu tattakin, inda suka bi su aguje, suka kamasu, suka lakada musu duka har suka kashesu.” Inji shi.

Babban likitan asibitin kwararru na jahar Gombe, Dakta Shuaibu Mu’azu ya tabbatar da amsan gawarwaki guda goma sha daya a asibitin, daga ciki har da na kananan yara guda 9 da kuma jami’an tsaron guda biyu.

Tuni mataimakin gwamnan jahar, Charles Iliya ya kai ziyara wannan Asibiti don duba wadanda suka jikkata, da kuma jajanta ma iyalan mamatan tare da kwantar musu da hankula game da abinda ya faru, sa’annan yayi alkawarin daukan nauyin kulawa da wadanda aka kwantar a Asibitin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel