Hukumar EFCC ta na binciken satar Biliyan 8.7 a JAMB

Hukumar EFCC ta na binciken satar Biliyan 8.7 a JAMB

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a Najeriya, ta fara gudanar da bincike a game da wasu kudi da ake zargi sun bace a hukumar JAMB daga shekarar 2010 zuwa 2016.

EFCC, Hukumar da ke yaki da masu wawurar kudin gwamnati tana kokarin gano yadda aka rika tafka sata a hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare kamar yadda Jaridar The Nation ta rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa EFCC za ta dura kan jami’an hukumar ta JAMB 15 wanda ake zargi da aikata ba daidai ba. Idan ba ku manta ba a 2018, wata Philomena Chieshe, tayu ikirarin cewa maciji ya hadiya Miliyan 36 na hukumar.

KU KARANTA: JAMB ta musanya jita-jitar fara saida fam a Najeriya

Hukumar EFCC ta na binciken satar Biliyan 8.7 a JAMB

Ana binciken wasu kudi su ka bace shekara 9 da su ka wuce a JAMB
Source: UGC

Bincike dai ya nuna cewa Naira Biliyan 8.7 da hukumar take tarawa a baya, ya kan kare ne a cikin aljihun wasu tsirarrun manyan ma’aikata. Jami’an na JAMB kan bada uzuri da hadarin mota, ko gobara ko kuma rikicin Boko Haram.

Daga cikin wadanda EFCC za ta biyo ta kan su akwai Philomena Chieshe, Sale Umar, Labaran TankoDaniel Agbo, Yakubu Jekada, Patricia Ogunsola da Cyril Izireim Imoukhuede. Saura sun hada da Murtala Abdul da Aliyu Yakubu.

Haka zalika daga cikin jihohin da wannan barna tayi kamari akwai irin su Benuwai, Nasarawa, Kano, Kogi, Filato, Gombe, Yobe da kuma jihar Edo. Yanzu dai EFCC ta bazama da nufin ganin ta gano inda aka rika kai wadannan tarin biliyoyi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel