Gobe za a tattare kudin Walter Onnoghen da ke cikin banki

Gobe za a tattare kudin Walter Onnoghen da ke cikin banki

Mun samu labari cewa a halin yanzu hukuma ta fara shirye-shiryen karbe makudan kudin da tsohon babban Alkalin Alkalan Najeriya Walter Onnoghen yake da su a cikin wasu akawun 5 a banki.

Sahara Reporters ta bayyana cewa za fara karbe dukiyoyin da tsohon Mai shari’a Walter Onnoghen ya bari ne a banki bayan kotun CCT mai kula da dukiya da kadarorin ma’aikatan gwamnati a Najeriya ta samu Alkalin da laifi.

Alkalin CCT ya samu Walter Onnoghen da laifin kin gabatarwa hukuma kudin da ya mallaka. Wannan ya sa aka tsige sa daga matsayinsa, sannan kuma aka karbe kudin da aka samu a cikin asusunsa, game da hana sa rike ofis.

Kotu ta bada umarni ne a karbe duk kudin da ke cikin asusun tsohon babban Alkalin kasar wanda hukuma ba ta san da zaman-su ba. Yanzu wannan kudi za su zama mallakar gwamnatin tarayya inji wani babban Lauya.

KU KARANTA: Atiku ya maidawa Lauyoyin Buhari martani game da salin sa

Gobe za a tattare kudin Walter Onnoghen da ke cikin banki

Kudin Walter Onnoghen za su shiga hannun Gwamnatin Najeriya
Source: Depositphotos

Umar Aliyu wanda yana cikin Lauyoyin da su ka maka Walter Onnoghen a gaban kotu, yace za su rubuta takarda inda za a nemi a rufe akawun din tsohon CJN din na bankin Standard Chartered, tare da kuma karbe duk kudin da ke ciki.

Babban Lauyan yace idan har ba a rubutawa banki da wannan bukata ba, ba za a iya samin damar karbe kudin da ke cikin akawun din na Walter Onnoghen ba. Ana kuma sa rai za a fara wannan shiri ne da zarar an gama hutu a kasar.

Yanzu haka dai an tafi hutun bikin Easter a Najeriya, amma CCT, ta bakin wani jami’in ta, Ibraheem Al-Hassan, ta tabbatar da cewa za a sanar da wadannan bankuna da su mikawa gwamnati kudin da Onnoghen ya bari ciki akawun din sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel