Yara da iyayensu na cin ganyen albasa a sansanin Bauchi saboda tsananin yunwa

Yara da iyayensu na cin ganyen albasa a sansanin Bauchi saboda tsananin yunwa

Rahotanni sun kawo cewa sakamakon halin rashin abinci da mazauna sansanin yan gudun hijira na jihar Bauchi ke ciki, a yanzu iyayen yara da yayansu sun koma ga cin ganyen albasa domin su rayu a wannan sansani.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wani mazaunin sansanin mai suna Ajidda Ahmed ya bayyana cewa wannan yunwa da suke fama da shi babu yaro ba ba babba ba.

Yace: “Babu wani dake kawo mana dauki a wannan sansani. Kowa ta kansa ya ke yi. Ya kaiga ganyen albasa dukkan mu muke ci domin mu rayu. Sannan dama can muna yin bahaya a daji ne gashi an shigo yanayi na damuna. Ruwan sha ma sai ya gagare mu. Abin ya zamo tashin hankali matuka yanzu.

Yara da iyayensu na cin ganyen albasa a sansanin Bauchi saboda tsananin yunwa

Yara da iyayensu na cin ganyen albasa a sansanin Bauchi saboda tsananin yunwa
Source: Facebook

Har ila yau wata mai suna Aisha Musa ta bayyana wa wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Bauchi cewa wahalar rashin abinci ya tsananta matuka a sansanin inda kowa ke dandana kudar sa.

KU KARANTA KUMA: Yadda ake fasa kaurin buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin Najeriya a kullun

Shugaban wannan sansani, Bulama Gojja, ya ce mazauna wanna sansani duk ‘yan kabilar shuwa-Arab ne da hare-haren Boko Haram ya fatattaka a kananan hukumomin Marte, Marfa da Marte, Marfa.

Gojja ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da kuma gwamnati da su kawo musu agaji saboda su kubuta daga wannan matsala da suka shiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel