Babu tsaro a Kaduna – Shehu Sani ya gargadi masu yawon shakatawa

Babu tsaro a Kaduna – Shehu Sani ya gargadi masu yawon shakatawa

Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya gargadi masu yawon bide ido da su kiyayi ziyartan jihar Kaduna.

Sanata Sani ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu, bayan kisan wata yar Birtaniya da wani kwararriya a fannin sadarwa a kamfanin Mercy Corps da sauran matafiya a ranar Asabar 20 ga watan Afrilu, a Kaduna.

Sanatan yace jihar Kaduna ba ta da tsaro ga masu yawon bude ido.

A cewar Sani, yan bindiga, masu garkuwa da kuma masu kisan matafiya da sauran masu yawon bude ido basu dauki kudirinsu da wasa ba.

Duk da haka, yayin da yake Allah wadai akan kisan, Sani ya mika jajensa zuwa ga iyalen wadanda lamarin ya cika dasu.

Ya bayyana cewa ana samun tashin hankali ne idan gwamnati ta gaza daukaka hakkinta na kare rayukan al’umma da kaddarorinsu, ko kuma idan tsarinta ya gaza.

KU KARANTA KUMA: Yadda ake fasa kaurin buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin Najeriya a kullun

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wadanda suka kashe yar Birtaniyan, Faye Mooney, wacce ta kasance jami’a a kamfanin Mercy Corps Nigeria, a jihar Kaduna sun nemi a basu kudin fansa har na naira miliyan 69 akan ma’aikata uku da aka sace.

An sace ma’aikatan uku ne a ranar Juma’a, 21 ga watan Afrilu a cibiyar shakatawa da ke yankin karamar hukumar Kujuru a jihar Kaduna.

An rahoto cewa mutane biyar ne aka sace amman biyu sun tsere. Wani majiyi a Kujuru yace yan bindiga biyar sunyi yunkurin shiga sansanin ta wata hanya dake a wata dutse dake kusa da sansanin bayan sunyi harbi a wajen shakatawar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel