Yan sanda sun samo makamai a sakatariyar PDP da APC a Kano, sun kama mutum 8

Yan sanda sun samo makamai a sakatariyar PDP da APC a Kano, sun kama mutum 8

Hukumar yan sanda a Kano ta samo wasu makamai a sakatariyar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke karamar hukumar Tudunwada na jihar da kuma sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Hakazalika, an kama yan bangan siyasa takwas da ke da nasaba da makaman, jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan, DSP Haruna Abdullahi ya bayyana.

Da yake tabbatar da lamarin, DSP Abdullahi yace makaman sun hada da takobi, adduna, wukake, da miyagun kwayoyi iri-iri da sauran makamai masu hadari wanda yan bangan siyasa ke amfani da su.

Yace kamun da samo makaman ya biyo bayan mamayar da yan sanda ke kaiwa mafakar masu laifi a jihar.

Yan sanda sun samo makamai a sakatariyar PDP da APC a Kano, sun kama mutum 8

Yan sanda sun samo makamai a sakatariyar PDP da APC a Kano, sun kama mutum 8
Source: UGC

Da aka kira shi, Shugaban APC a jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ya karyata kamun kowani mamba na APC sannan yace babu wani dan jam’iyyar da ke da nasaba da makaman da aka samo.

KU KARANTA KUMA: Yadda ake fasa kaurin buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin Najeriya a kullun

A nashi martanin, sakataren PDP, Alhaji Shehu Wada Sagagi yace babu wanda ya kai rahoton lamarin sakatariyar jam’iyyar na jihar.

Sagagi ya tabbatar da cewa an saki mambobin PDP da aka kama akan beli yayinda yan sanda basu samu komai na laifi a tattare da su ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel