Yarbawa ne za su samar da Shugaban kasa na gaba a 2023 - Afenifere

Yarbawa ne za su samar da Shugaban kasa na gaba a 2023 - Afenifere

Gamayyar kungiyar Afenifere, a jihar Ekiti a jiya, Lahadi, 21 ga watan Afrilu sun nuna yakinin cewa kasar Yarbawa ce za ta samar da Shugaban kasar Najeriya na gaba a shekarar 2023.

Da yake jawabi ga manema labarai a Ado-Ekiti, jagoran kungiyar na jihar, Mista Bunmi Awotiku ya bayyana cewa kungiyar za ta taka muhimmiyar rawar gani wajen gangamin ajandar kasar Yarbawa a 2023.

Yace: "Yankin kudu maso yamma ta dade tana ba gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari gudunmawa na manufofi da shirye-shirye sannan kuma za mu ci gaba da yin hakan. Muna so ya cimma nasara kuma da izinin Allah zai cimma nasara.

Yarbawa ne za su samar da Shugaban kasa na gaba a 2023 - Afenifere

Yarbawa ne za su samar da Shugaban kasa na gaba a 2023 - Afenifere

“Za mu yi zaman tattauanawa kuma ina iya ba ku tabbacin cewa Yarbawa za su fuskanci alkibla guda a wannan lokacin. Mun koyi darasinmu a matsayin mutane sannan kuma ba za su bari rikicin cikin gida ya hana mu samun wannan babban garabasa ba irin na shugabancin kasa.”

KU KARANTA KUMA: Matasa na iya hana mu manyan mutane fita nan da shekara 5 - Dangote

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, Kungiyar matasan arewa karkashin inuwar Arewa Youth Forum (AYF), a jiya, Lahadi, 21 ga watan Afrilu sun zargi babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu da mayar da kansa mai zartarwa a cikin jam’iyyar.

Da suke martani akan jayayyar da ke faruwa game da shugabancin majalisar dokokin kasar a wani jawabi a Kaduna, kungiyar AYF tace yunkurin da Tinubu ke yin a tursasa wanda ya ke murai akan mambobin majalisar dokokin kasar ya saaba ma damokradiya da kuma ra’ayin arewa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel