Matasan arewa sun yi wa Tinubu wankin babban bargo kan shugabancin majalisa

Matasan arewa sun yi wa Tinubu wankin babban bargo kan shugabancin majalisa

Kungiyar matasan arewa karkashin inuwar Arewa Youth Forum (AYF), a jiya, Lahadi, 21 ga watan Afrilu sun zargi babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu da mayar da kansa mai zartarwa a cikin jam’iyyar.

Da suke martani akan jayayyar da ke faruwa game da shugabancin majalisar dokokin kasar a wani jawabi a Kaduna, kungiyar AYF tace yunkurin da Tinubu ke yin a tursasa wanda ya ke murai akan mambobin majalisar dokokin kasar ya saaba ma damokradiya da kuma ra’ayin arewa baki daya.

Jawabin dauke da sa hannun Shugaban kungiyar na kasa, Gambo Ibrahim Gujungu da daraktan harkokin jama’a na kungiyar, Bello Abdulhamid sunce, “ga duk wani mai tunani da lura sosai, wannan lamari ya nuna Bola Tinubu a matsayin mara kishin arewa kuma mai son kai don samar da hanyar da zai dunga jan ragamar APC da kuma zartar da hukunci a madadin Shugaban jam’iyyar, duk don gina zaben 2023.

Matasan arewa sun yi wa Tinubu wankin babban bargo kan shugabancin majalisa

Matasan arewa sun yi wa Tinubu wankin babban bargo kan shugabancin majalisa
Source: Facebook

“Muna kuma farin ciki da jawabin da aka ce jigon jam’iyyar yayi inda yace jami’an jam’iyyar da basa farin ciki da zabin da kuma tursasawar da ake on yi masa da wasu jami’an jam’iyyar suna iya barin APC.

KU KARANTA KUMA: Tsagwaron kishi: Wani magidanci, Danjuma ya kashe matar sa saboda ta ce za ta sake aure idan ya mutu

“Don haka muna ganin hakan bai dace da jigo na kasa ba. Kuma, mun yi imanin cewa wannan tursasawan ya saba ma damokradiya, ya saba ma da’a, sannan ya saba ma koyarwa nagari."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel