Yanda Najeriya zata fuskanci tallafin man fetur

Yanda Najeriya zata fuskanci tallafin man fetur

-Halin tsaka mai wuya, shi Najeriya ke ciki kan sha'anin tallafin man fetur saboda tabbas tana kashe kudade masu yawa wajen biyan kan tallafin man

-Shin idan aka janye wannan tallafin mai, ko menene zai biyo baya?

Matsin lamba daga wurin kungiyar kudin ta duniya wato IMF akan gwamnatin Najeriya na ta janye tallafin man fetur ya janyo tsawon layuka a gidajen man kasar nan. Wannan al’amari ya sanya gwamnatin cikin hali na tunanin ya zatayi da wannan matsala.

Jogarar ta IMF, Christine Lagarde itace tayi wannan kiran a makon jiya inda tace, janye tallafin shine abu mafi dacewa a halin yanzu. Yayinda take zantawa da yan jarida jim kadan bayan kammala wata ganawa ta musamman da akeyi ko wace shekara da bankin duniya, a birnin Washington DC. Tace yana da matukar muhimmanci ga kasar na ta janye tallafin domin tayi amfani da kudin wurin bunkasa kula da lafiya, ilimi, gine-gine da ma wasu abubuwan.

Yanda Najeriya zata fuskanci tallafin man fetur

Lagarde, Baru da Kachikwu
Source: UGC

KU KARANTA:Kotun hukumar kiyaye hadurra (FRSC) ta Kano ta gurfanar da mutum 32 a gabanta lokacin bikin ista

“ Idan kuka duba kudaden da ake kashewa akan tallafin kacal sun kai dala tiriliyan biyar da digo biyu ($5.2tn). Idan da ace za’a janye tallafin zai kasance an samu kudin da zai yi amfani wajen gina tituna, gyara asibitoci, gina sabbin makarantu dama bunkasa hanyar bayar da ilimin kanta,” a cewar shugabar IMF.

Jim kadan bayan jawabin na Lagarde, da take maida jawabi a wurin ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed, tace bamu da wani shiri na janye tallafin man a halin yanzu. Ga kadan daga cikin abinda take cewa: “Bamu da shirin janye tallafin man a yanzu, dalili kuwa shine saboda bamu shiryama abinda zai biyo bayan yin hakan ba.

Ya zama dole mu fahimtar da mutanenmu akan yin hakan idan har ya zama dole, sannan kuma zamu cigaba da tuntubar kungiyoyi daban-daban domin samun mafita kan wannan lamari. Saboda haka a halin yanzu dai zancen janye tallafin man baya gabanmu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel