An gano wace ce baturiyar da masu garkuwa suka kashe a Kaduna

An gano wace ce baturiyar da masu garkuwa suka kashe a Kaduna

An gano wace ce baturiyar da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka kashe a karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

An bayyana cewar matar mai suna Faye Money, 'yar asalin kasar Ingila ce da ke aiki da wata kungiya (Mercy Corps Nigeria) a Najeriya.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ne ya bayyana hakan a dandalin sadar wa na WhatsApp mallakar rundunar 'yan sanda, ya ce rundunar 'yan sanda na yin iya bakin kokarinta domin kubutar da ragowar mutanen da aka sace tare da kama masu garkuwa da su domin su fuskanci hukunci.

A cewar Sabo; "mu na cigaba da kokari har yanzu domin kubutar da dukkan ragowar da aka sace tare da kama masu laifin.

An gano wace ce baturiyar da masu garkuwa suka kashe a Kaduna

Faye Money
Source: Twitter

"Mun gano cewar matar da aka kashe sunanta Faye Money kuma 'yar kasar Ingila ce. Ma'aikaciya ce a 'Mercy Corps Nigeria'. Mu na cigaba da bincike a kan yadda aka kashe ta," a rubutaccen sakon da kakakin ya wallafa.

A ranar juma'a ne wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai harin 'kan mai uwa da wabi' da misalin karfe 11:30 na safe a Kajuru, 'yan bindigar sun bude wuta a kan jama'a bayan dirar su.

DUBA WANNAN: Wani magidanci, Danjuma ya kashe matar sa a kan ta ce za ta sake aure idan ya mutu

Wata majiya mai kusanci da shugaban karamar hukumar Kajuru ta shaida wa majiyar mu cewar masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da mutane biyar. Wata majiyar ta ce an yi wani taro a Kajuru a daren safiyar da masu garkuwar suka diro garin.

Majiya ta bayyana cewar, "tabbas an kawo hari Kajuru amma mu na zargin masu garkuwa da mutane ne, kuma sun kashe wata baturiya da bamu san daga ina ta fito ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel