Tsagwaron kishi: Wani magidanci, Danjuma ya kashe matar sa saboda ta ce za ta sake aure idan ya mutu

Tsagwaron kishi: Wani magidanci, Danjuma ya kashe matar sa saboda ta ce za ta sake aure idan ya mutu

Wani maigidanci mai suna Uwani Danjuma, mai shekaru 30 a duniya, ya kashe matar sa saboda ta bayyana masa cewar idan ya mutu za ta sake yin wani auren.

Lamarin ya faru ne a kauyen Uddu da ke karamar hukumar Rijau a jihar Neja.

A cewar Danjuma, matar sa ta fada masa a lokacin da bashi da lafiya, wasu makonni da suka wuce, cewar za ta sake yin aure idan ya mutu.

Kalaman matar basu yiwa Danjuma dadi ba, hakan kuma ya sa shi yin amfani da wata sharbebiyar wuka wajen kashe ta bayan ya warke.

Da yake amsa laifinsa, Danjuma ya bayyana cewar ya kashe matar sa ne lokacin da take bacci saboda jin haushin kalaman da ta fada masa lokacin da bashi da lafiya.

Tsagwaron kishi: Wani magidanci, Danjuma ya kashe matar sa saboda ta ce za ta sake aure idan ya mutu
Danjuma
Source: Twitter

"Ban yi tunanin mata ta za ta iya fada min cewar za ta sake yin aure ba idan na mutu. Bacin rai ne ya sa na ji mata ciwo da wuka a wuya kuma ya zama silar mutuwar ta.

"Ni ban yi nadamar kashe ta ba saboda ita ma so take na mutu, na kashe ta ne saboda kar ta sake yin wani auren. Bai kamata ta fada min hakan a kunne na ba, gara ta tafi lahira, inda Allah zai saka ta a wuta saboda rashin iya kama harshenta," a cewar Danjuma

DUBA WANNAN: Hotunan kafin aure na ango mai shekara 17 da amaryarsa mai shekara 15 a Sokoto

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Neja, Mohammad Abubakar, ya bayyana cewar sun kama mai laifin ne bayan samun labarin abinda ya faru, ya kara da cewa Danjuma ya amsa laifinsa da kan sa.

Abubakar ya kara da cewa raunin da Danjuma ya yiwa matar sa a wuya ne ya zama sanadin mutuwar ta, ya kara da cewa za su gurfanar da mai laifin a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel