Kashi 80 cikin dari na ma’aikatan jihar Sakkwato na goyon bayanmu, inji Jagoran jam’iyar APC na jihar

Kashi 80 cikin dari na ma’aikatan jihar Sakkwato na goyon bayanmu, inji Jagoran jam’iyar APC na jihar

-Magoya bayan jam'iyar APC daga cikin ma'aikatan jihar Sakkwato na cikin tsaka mai wuya

-Shin ko ma'aikatan Sakkwato na cikin farin ciki dangane da zababben gwamnansu?

Jam’iyar ta APC reshen jihar Sakkwato ta bayyana cewa sama da kashi 80 cikin dari na ma’aikatan jihar na goyon bayanta. Jagoran jam’iyar mai suna Isa Sadiq Achida ne yayi wannan magana ranar Lahadi a jihar Sakkwato.

Achida wanda shine shugaban jam’iyar ta APC a jihar Sakkwato yace, abinda ya biyo bayan zaben gwamna a jihar dangane da ma’aikatan da suka zabesu muzgunawace daga wajen gwamnatin jihar wacce Aminu Tambuwal ke jagoranta.

Kashi 80 cikin dari na ma’aikatan jihar Sakkwato na goyon bayanmu, inji Jagoran jam’iyar APC na jihar

APC Logo
Source: UGC

KU KARANTA:Tsohon shugaban kasar Kenya ya rasa dansa na farko

Shugaban jam’iyar ta APC da yake gabatar da wata takarda mai taken, ‘cin zarafin siyasa a tsakanin ma’aikatan jihar Sakkwato’. Ya koka da cewa duk ma’aikatan da suka zabi jam’iyarsu an hanasu albashinsu tare kuma sauya musu wurin aiki.

Bugu da kari, shugaban jam’iyar ya kara da cewa, harma wasu daga cikin hakkokan jama’a da ya kunshi ruwan sha, hanasu wurin kasuwanci a kasuwa da kuma wasu abubawa da dama na matsi da takura sun biyo baya ga magoya bayan jam’iyar APC bayan da aka kammala zabe.

“Ko shakka babu, sama da kashi 80 na ma’aikatan jihar nan na tausayawa jam’iyarmu. Kuma kowa ya sani suna yin aikinsu ne tsakaninsu da Allah domin cigaban gwamnati dama jihar Sakkwato baki daya. Duk wani matsi ga ma’aikatan ba zai haifar da komai ba sai rashin cigaba a al’amuran jihar baki daya.”

Sadiq ya sake cewa, jam’iyar tasu zata bi duk wasu hanyoyi da suka dace a shari’ance domin kwatowa wadannan ma’aikata hakkinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel