Sarkin Kano yace yunwa da rashin tsaro sun yi katutu a Arewacin Najeriya

Sarkin Kano yace yunwa da rashin tsaro sun yi katutu a Arewacin Najeriya

A makon da ya gabata ne aka shirya taro na musamman domin tunawa da Marigayi Malam Aminu Kano wanda ya rasu shekaru 36 da su ka wuce a Najeriya. Sarki Muhammadu Sanusi yayi jawabi a taron.

Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya koka a game da yadda yunwa da talauci su ka dabaibaye Arewacin kasar nan inda yace duk kasar da ta samu kan-ta a irin wannan mawuyacin hali, lallai ta shiga cikin babbar matsala.

Sarkin na Kano yayi tsokaci ne a game da wata takarda da tsohon shugaban kungiyar Lauyoyin Najeriya na NBA, AB Mahmood ya gabatar a wajen wannan taro da aka shirya a gidan Mambayya House a Ranar Laraba, 17 ga Watan Afrilu.

Mai Martaba yake cewa duk da yunkurin dabakka shari’a a wasu jihohin Arewa, sai dai Arewacin Najeriyar na cikin wani halin matsi na tattalin arziki. Wannan ya sa Sarkin ya nemi ya kawo dokokin da za su gyara al’umma a Kano.

KU KARANTA: Abin da ya sa Najeriya ba za ta gyaru ba - Sarkin Kano

Dokokin da za a kawo za su kawo gyara wajen harkar zaman aure da barace-barace da almajiranci. Sarki yake cewa masu mulki sun fi karkata ne wajen harkar yanke hukunci watau haddi na musulunci wajen aiwatar da shari’a.

A jawabin Sarkin ya bayyana cewa Barawon Gwamnati yana yi wa jama’a illar da ta ribanya ta Barawon akuya, don haka yace akwai bukatar a sake duba lamarin shari’a da wata mahangar domin ganin an shawo kan matsalolin Arewa.

Alkaluman Oxford Human development indicators na shekarar 2015 sun nuna cewa kashi 20% na mutanen Kudu maso yamma ne ke cikin talauci yayin a Arewa ta yamma ake fama da kashi 80% duk su na fama da taluci inji Sarkin na Kano.

KU KARANTA: Kudi ne ke aiki a zaben Najeriya yanzu- Tsohon Sakataren Gwamnati

Sarkin yake cewa idan har ba a sake duba dokokin aure, da zaman iyali, da sha’anin saki ba, dole Arewa za ta cigaba da ciran tuta wajen ta’addanci da shaye-shayen kwayoyi, da garkuwa da mutane, da matsalar Almajiranci da dabar siyasa.

A nan da shekaru 20 zuwa 30 masu zuwa, Sanusi II yace Arewa za tayi fama da rikicin da ya fi na yau saboda ganin yadda ake da Almajirai miliyan 3 su na gara-ramba a Kano, wanda a cikin su babu wanda zai iya zama Likita ko Alkali nan gaba.

Duk a jawabin Sarkin, ya koka da yadda Malami ke tsoma kan su cikin sha’anin siyasa inda yace kamata yayi a maida hankali kan Ilmin yara da kiwon lafiya a maimakon a rika kai Malamai yawon Umrah da Hajji da sauran su idan ana so a cigaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel