Kwamitin koli na Shari'a ya yi tir FG, ya yi kaca-kaca da Buhari

Kwamitin koli na Shari'a ya yi tir FG, ya yi kaca-kaca da Buhari

- Kwamitin koli na shar'ar Musulunci (SCSN) ya soki salon rikon da gwamnati tarayya ta yiwa matsalar rashin tsaro

- Kwamitin ya yi kira ga gwamnati da ta canja salon yakin da take yi da kalubalen tsaro da ke damun Najeriya

- SCSN ta kara da cewa salon da gwamnati ke amfani da shi ba zai samar da zaman lafiyar da ake bukata ba, ta ce akwai bukatar ake bibiyar kwazoon shugabannin rundunonin tsaro

Kwamitin koli na shari'ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ya yi tir da gwamnatin tarayya a kan rikon sakainar kashin da take yiwa matsalar rashin tsaro a sassan kasar nan.

A wata sanarwa da sakataren ta, Nafiu Baba Ahmad, ya fitar bayan taron kwamitin a kan azumin watan Ramadana, SCSN ta shawarci gwamnatin tarayya a kan ta canja salon yadda take yaki da kalubalen tsaro.

Kwamitin koli na Shari'a ya yi tir FG, ya yi kaca-kaca da Buhari

Kwamitin koli na Shari'a ya yi tir FG, ya yi kaca-kaca da Buhari
Source: Twitter

Da yake karanta jawabin ga manema labarai, shugaban SCSN, Dakta Ibrahim Datti Ahmad, kwamitin ya bayyana cewar matakan da gwamnati ke dauka ba zasu samar da tsaron da ake bukata ba.

DUBA WANNAN: Benuwe: 'Yan bindiga sun bude wuta a kan ibada, sun kashe mutane 11

SCSN tayi kira ga gwamnata da ta sake duba tsare-tsaren da take amfani da su domin ta sauke nauyin da ke kan ta na kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu. Kazalika ta shawarci gwamnatin da ta ke bibibiyar kwazon shugabannin rundunonin tsaro domin sanin yadda suke gudanar da aiyukansu da sarrafa hukumominsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel