Bayan hutun 'Easter' za mu saki sakamakon jarrabawa - JAMB

Bayan hutun 'Easter' za mu saki sakamakon jarrabawa - JAMB

Hukumar gudanar da harkokin jarrabawar neman shiga jami'o'i JAMB, ta ce a nan ba da jimawa ba za ta sadar da sakonni ta hanyar wayar salula ga dalibai domin sanar da su a kan lokacin da za ta saki sakamakon jarrabawar bana.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, hukumar JAMB ta ce a kwana-kwanan nan za ta tura sakonni ga dalibai masu neman shiga jami'o'i domin sanar da su a kan lokacin da za ta saki sakamakon jarrabawar bana da zarar ta kammala tantancewa.

Bayan hutun 'Easter' za mu saki sakamakon jarrabawa - JAMB

Bayan hutun 'Easter' za mu saki sakamakon jarrabawa - JAMB
Source: Depositphotos

Shugaban sadarwa na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata hira yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Lahadi cikin birnin Legas.

A cewar sa, Dakta Benjamin ya nemi dalibai da su kauracewa sauraron jita-jitar masu yada kanzon kurege da rade-radin a kan sakamakon jarrabawar bana musamman a kafofi da dandalan sada zumunta.

KARANTA KUMA: Masu Garkuwa da Mutane sun kashe Mutane 2 a Kaduna da Mutane 11 a jihar Benuwai

Rahotanni sun bayyana cewa, fiye da dalibai miliyan 1.8 masu neman shiga jami'o'i sun zana jarrabawar JAMB ta bana cikin dukkanin jihohi da ke fadin kasar nan daga ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu zuwa ranar Laraba, 18 ga watan Afrilun 2019.

Hukumar JAMB bisa jagorancin Farfesa Ishaq Oloyede, ta yaba da salo, tsari da kuma yanayi na gudanar da jarrabawar bana da a cewar ta ta tsarkaka daga ababe na magudi ko kuma kalubale sabanin yadda ta kasance a baya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel