2019: Ba zabe aka yi a Najeriya ba, kudi ne yayi aiki inji Cif Olu Falae

2019: Ba zabe aka yi a Najeriya ba, kudi ne yayi aiki inji Cif Olu Falae

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Olu Fale, yayi Allah-wadai da zaben 2019 da aka yi kwanan nan. Olu Falae da yake hira da Jaridar The Sun kwanan nan, yace sam ba zabe aka yi a zaben bana ba.

Kamar yadda Jaridar ta The Sun ta wallafa a bugun ta na Ranar Lahadi, Cif Olu Falae ya bayyana cewa sayen kuri’a kurum ‘yan siyasa su ka rika yi kiri-kiri a maimakon a bari mutane su yi amfani da ra’ayin su wajen kada kuri’a.

Olu Falae ya koka da yadda kudi ke tasiri wajen zabe inda ya kuma ce ‘yan siyasa sun daina kawowa mutane manufofinsu a lokacin da ake yakin neman zabe. Falae yace a halin yanzu wanda ya fi kudi, shi yake cin zabe a Najeriya.

Falae yace muddin kudi ne zai rika aiki wajen zaben shugabanni, kasar ba za ta samu ‘yan siyasa masu akida da manufa da za ta mulke ta ba. Tsohon SGF din kasar yace yanzu an sauka daga kan turbar siyasar yi wa al’umma bauta.

KU KARANTA: Maganganun Shugaban INEC zai jefa Malaman Najeriya cikin matsala

2019: Ba zabe aka yi a Najeriya ba, kudi ne yayi aiki inji Cif Olu Falae

Tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya ya soki zaben bana
Source: Depositphotos

Cif Falae ya nuna cewa babu shakka sai da kudi ake takara kamar yadda ya kashe sama da Naira Miliyan 600 a zaben 1999 wajen buga hotuna da yawon kamfe. Sai dai Falae yace bai kashe taro wajen sayen kuri’a ko wajen murde zabe ba.

Tsohon ‘dan siyasar yake cewa a yanzu masu fitowa takara su kan ware kudi domin sayen kuri’ar Talakawa, sannan kuma a kan biya Ma’aikatan zabe na INEC da kuma jami’an tsaro makudan kudi domin a tafka magudi a zaben kasar.

Dazu kun ji cewa Atiku Abubakar ya dauko hayar manyan Lauyoyi irin su Dr. Livy Uzoukwu da Kabiru Tanimu Turaki, Chris Uche, Emeka Etiba, da su Mike Ozekhome. domin karbe nasarar da shugaba Buhari yayi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel