Benuwe: 'Yan bindiga sun bude wuta a kan ibada, sun kashe mutane 11

Benuwe: 'Yan bindiga sun bude wuta a kan ibada, sun kashe mutane 11

- Riikici tsakanin wasu kabilu biyu a jihar Benuwe ya dauki sabon salon da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11

- An kashe mutane 11 ne a hanyar su ta dawowa daga coci

- An tsaurara tsaro a yankin da abin ya faru domin tabbatar da zaman lafiya

Rikicin kabilanci tsakanin wasu kabilu a jihar Benuwe ya dauki sabon salo bayan wasu 'yan bindiga sun bude wuta a kan wasu mabiya addini kirista a kauyen Tse-Aye da Tse-Ngibo da Ikurav Tiev da ke karkashin karamar hukumar Katsina Ala.

Jaridar Vanguard ta ce an kai harin ne sakamakon gabar da ke tsakanin mutanen garin Shitile da na kauyukan Sankera da suka hada da Logo, Ukum da wasu kauyukan karamar hukumar Katsina Ala.

Wani babban jami'in gwamnati da bai yarda a ambaci sunansa ba ya ce duk kokarin sulhunta mutanen kauyukan ya ci tura.

Benuwe: 'Yan bindiga sun bude wuta a kan ibada, sun kashe mutane 11

Gwamnan jihar Benuwe: Samuel Ortom
Source: UGC

A cewar sa, "tun a farkon shekarar na wasu 'yan tada zaune tsaye daga kauyen Shitile suka kai hari kauyen Ikurav tare da kashe mutane 10. Dattawan gari da shugaban karamar hukumar sun shiga maganar, sun gargade su a kan kai harin daukan fansa.

"Wannan karon kuma jama'ar da suka je coci yin ibadar bikin yista ranar juma'a aka kai wa harin kwanton bauna a hanyar su ta dawowa gida. 'Yan bindigar sun tare musu hanya ne a kauyukan Tse-Ngibo da Tse-Toraye, inda suka kashe mutane 11, wasu kuma da dama suka bazama cikin daji, har yanzu ba a gansu ba.

DUBA WANNAN: Kuma dai: 'Yan bindiga sun yiwa mutane 16 kisan wulakanci a Zamfara

"Ya zuwa yanzu dai ba a san takamaiman adadin mutanen da suka kashe ba tunda ba a san inda kusn mutane 40 suke ba.

"Bayan sun kashe mutanen, sun dauke motar daya daga cikin mutanen da suka mutu sannan sun tafi da shanu da yawa daga kauyukan."

Manjo Janar Adeyemi Yekini, kwamandan atisayen yaki da 'yan bindiga a jihar Benuwe, ya tabbatar da kai harin.

Ya ce tuni an tura karin dakarun soji zuwa yankin domin tabbatar da tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel