Kazaman ‘Yan siyasa za su batawa Malamai suna – inji Sanata Shehu Sani

Kazaman ‘Yan siyasa za su batawa Malamai suna – inji Sanata Shehu Sani

- Shehu Sani ya nemi Malaman jami’o'i su fita daga harkar zabe

- Sanatan yana gani wannan ne zai tsira da mutuncin makarantu

Labari ya iso gare mu cewa fitaccen Sanatan nan na Arewacin Najeriya wanda yayi fice watau Kwamared Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa a game da zargin da ake yi wa Malaman jami’a na taimakawa wajen murde zaben bana.

Sanatan yayi tsokaci ne a kan jawabin da tsohon shugaban hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta, watau Farfesa Attahiru Muhammad Jega, yayi kwanaki inda yace an yi amfani da wasu Malaman jami’a wajen tafka magudin zabe a bana.

KU KARANTA: Kotu ta warware gardamar 'Ya 'yan PDP a Jihar Kano

Kazaman ‘Yan siyasa za su batawa Malamai suna – inji Sanata Shehu Sani

Shehu Sani yayi tsokaci a kan maganar Farfesa Jega
Source: Depositphotos

Sani ya nemi a dakatar da Malaman jami’o’in Najeriya daga shiga cikin harkar zabe domin su rufawa kan su asiri, su tsira da ragowar mutuncin da ya rage masu. Sanatan yana ganin cewa ‘yan siyasa za su batawa Malaman suna.

‘Dan majalisar dattawan kasar yake ganin wannan ya sa ya zama dole Malaman jami’o’i su zare hannun su daga harkar zabe domin gujewa abin da zai jawo masu bakin jini da bacin suna daga kazaman ‘yan siyasan da ake da su.

Sanatan mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PRP mai adawa yayi wannan kira ne a shafin sa na sada zumunta kamar yadda ya saba. Sani yace janye jikin Malamai shi ne zai sa Makarantu su tsira da sauran mutunci.

“In the light of the new revelations, University lecturers should pull out from participating in the conduct of national elections to save the reputation & protect the moral sanctity of the academia. The Ivory tower shouldn’t be smeared with political faeces.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel