Masu Garkuwa da Mutane sun kashe Mutane 2 a Kaduna da Mutane 11 a jihar Benuwai

Masu Garkuwa da Mutane sun kashe Mutane 2 a Kaduna da Mutane 11 a jihar Benuwai

Bayan hallaka Mutane biyu ta hanyar harbin harsahin bindiga da sanyin safiyar ranar Asabar , masu ta'adar garkuwa da Mutane sun kuma yi awon gaba da Mutane uku a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Masu Garkuwa da Mutane sun kashe Mutane 2 a Kaduna da Mutane 11 a jihar Benuwai
Masu Garkuwa da Mutane sun kashe Mutane 2 a Kaduna da Mutane 11 a jihar Benuwai
Source: Twitter

Kazalika 'yan ta'adda rike da makamai na bindigu, sun hallaka Mutane 11 cikin kauyukan Ndigbo da kuma Tse-Aye na gundumar Ikyurav-Tive ta karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benuwai a ranar ta Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharan bayan hallaka Mutane 4 a kauyen Ndigbo da kuma 11 a kauyen Tse Aye na jihar ta Benuwai, sun kuma yi awon gaba a kimanin shanu 28 mallakin wani mutum, Agwaza Atedze.

A yayin haka kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari da ya janyo salwantar rayukan wasu baki biyu masu yawon buda ido 'yan jihar Legas da suka hadar da Mace guda.

KARANTA KUMA: An kashe babban Limami a jihar Jigawa, an yi masa fashi na N400,000

Kakakin 'yan sandan jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, ta bayar da shaidar aukuwar ta'addancin kan al'ummar jihar da ta sanya da dama a halin yanzu sun tsere daga muhallan su domin neman mafaka.

Bayan da tarzoma ta lafa cikin garuruwan biyu, rundunar 'yan sanda ta daura damarar bankado masu hannu cikin wannan miyagun laifuka tare da shan alwashin hukunta su daidai da abin da suka aikata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel