Hukumar NDLEA ta cafke Mutane 2 da hodar Iblis a jihar Kano

Hukumar NDLEA ta cafke Mutane 2 da hodar Iblis a jihar Kano

Hukumar hana ta'ammali da miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu Mutane biyu da mallakin hodar iblis mai nauyin kilo 2.927 kamar yadda kafar watsa labarai ta jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Hodar Iblis

Hodar Iblis
Source: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kwamandan hukumar na jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai. Ya ce an cafke ababen zargin biyu a wani Otel cikin birnin Kano daura da hanyar jihar Katsina.

Ya ce hukumar bayan shafe tsawon lokuta na sanya idanun lura a kan ababen zargin biyu sakamakon wani rahoto na leken asiri, ta samu nasarar cafke su suna tsaka da hadidiye mummunan kayan na maye da manufa ta shiga da su kasar Saudiyya inda za su yi shataletale da kasar Sudan.

Babban jami'in ya ce hukumar ta samu nasarar cafke ababen zargin biyu, Abdul Abubakar da Ibrahim Mustapha, a sakamakon matsin lamba da kuma tsayuwar daka ta fafutikar kawo karshen fatauci da kuma ta'ammali na miyagu kwayoyi a jihar Kano.

KARANTA KUMA: Abubuwa 5 game da Sarauniyar Ingila yayin da ta cika shekaru 93 a duniya

Kazalika hukumar NDLEA ta cafke wasu mutane hudu tare da mallakin bindiga ta sakayawa cikin aljihu daura da hanyar garin Gwarzo a kan hanyar su da zuwa karamar hukumar Funtuwa da ke jihar Katsina.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel