Jarumi Adam Zango ya kammala shirin angonce wa a karo na shida

Jarumi Adam Zango ya kammala shirin angonce wa a karo na shida

Adam A. Zango, jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ya kammala shiti tsaf domin angonce wa a karo na shida cikin shekara 13.

A katin gayyatar daurin auren da majiyar mu ta gani da idonta, Zango zai angonce da wata mai suna Safiya Umar Chalawa, wacce aka fi kira da Suffy, a ranar juma'a mai zuwa da misalin karfe 2:30 na rana.

Za a daura auren ne a masallacin fadar sarkin Gwandu da ke garin Gwandu, a jihar Kebbi.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar Zango ya yi aure sau biyar a baya, ya samu 'ya'ya shida; hudu maza, biyu mata, daga mata biyar da ya aura kafin su rabu.

Amina ce matar Zango ta farko da ya aura a shekarar 2006. Ita ce uwar yaron sa na farko, Haidar, wanda yanzu haka ya cika shekara 12 da haihuwa. Majiyar mu ta ce ba ta san abinda ya raba auren Zango da Amina ba.

Jarumi Adam Zango ya kammala shirin angonce wa a karo na shida

Jarumi Adam Zango da wasu daga cikin iyalinsa
Source: UGC

Zango ya kara auren wata matar mai suna A'isha, 'yar asalin Shika ta karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna. Ta haifa masa 'ya'ya maza uku.

Jarumin ya auri matar sa ta uku mai suna Maryam daga jihar Nasarawa.

Daga bisani ya auri wata jarumar fim mai suna Maryam AB Yola a Lugbe, Abuja a shekarar 2013. Sun bayyana tare a cikin wani shirin fim din Hausa mai suna 'Nas'

DUBA WANNAN: Adam Zango ya shiga rigima da fitaccen jarumin Kannywood a kan zagin mahaifiyar sa

A shekarar 2015, Zango ya auri Ummul Kulsum daga Ngaoundere a jamhuriyar Kamaru. An yi auren a sirrance. Ummul Kulsum ce ta fara haifa wa Zango diya mace, wacce ya sanya wa suna Murjanatu.

Safiyya ko kuma Suffy kamar yadda ake kiranta, ita ce za ta kasance matar Zango ta shida da ya aura.

Majiyar mu ta ce Zango ya saki dukkan mata biyar da ya aura a baya, sai dai har yanzu ba ta san dalilin rabuwar sa da matan da ya ke aura ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel