Zababben senata ya roki gwamnati da ta karasa aikin hanyar zuwa tashar Baro

Zababben senata ya roki gwamnati da ta karasa aikin hanyar zuwa tashar Baro

-Kammala titin Baro zai yi matukar habbaka tashar, ba tare da cikas ko tsaiko ba musamman wurin kaiwa da komowa

-Hanyar dai ta Baro ta faro ne daga Agaie inda ta ratsa Katcha zuwa Baro inda tashar jirgin take

Zababben senatan mai suna Alhaji Muhammad Bima Enagi wanda ke wakiltar Neja ta kudu ya roki gwamnatin tarayya da ta kammala hanyar zuwa tashar jirgin ruwa ta Baro. Hanyar da ta fara daga Agaie zuwa Baro dai an dakatar da aikinta ne da dadewa.

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust ranar Lahadi a Minna, zababben senatan ya jinjinama gwamnatin tarayya bisa kokarin da tayi na kammala aikin gina tashar jirgin ruwan a Baro. Amma sai dai ya kara da cewa wannan tasha za’a iya amfani da ita ne kawai idan aka kammala wannan hanyar.

Zababben senata ya roki gwamnati da ta karasa aikin hanyar zuwa tashar Baro

Hanyar tashar Baro
Source: UGC

KU KARANTA:Bayan shekara 18 da aure, wata mata ta haifi yara 5 a jihar Kogi

Aikin wannan hanyar dai, an bada shi ne a shekarar 2009 sai dai kuma an sake karbe wannan aiki a shekarar 2012 kamar yanda jaridar Daily Trust ta shaida mana. Dalilin kuwa da yasa aka karben aikin ya kasance ne saboda sakacin dan kwangilar da aka baiwa aikin wanda ya kasa cika alkawarin kammala aikin a lokacin da ya dace.

Bugu da kari, a shekarar 2015 gwamnatin tarayya ta sake bayar da kwangilar wannan aiki da tsawon titin ya kama kilomita 28.7 ga wani kamfanin Indiya akan kudi naira biliyan sha bakwai da miliyan dari biyar (N17.5bn) wanda zai dauki tsawon wata 12 kan a gama.

Mnistan ayukka a wancan lokacin, Mike Onolememen ya ke cewa yayin kaddamar da wannan aiki, niyyar gwamnatin tarayya itace ta bunkasa tattalin arzikin arewacin kasar nan ta hanyar bude wannan tasha a Baro. Amma sai ya zamana an samu cikas wajen fitar da kudin yin wannan aiki.

Bima ya kara da cewa, akwai matukar bukata na a kammala wannan titi domin yin hakan zai bada damar gudanar da harkokin da suka shafi wannan tashar ba tare da wani cikas ba ko kuma wani abin da kan iya zama koma baya. A karshe ya sake yabawa gwamnatin Buhari na kokarinta wajen ganin cewa ta kammala kuma anyi bikin bude wannan tasha.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel