Hukumar 'yan sanda ta cafke makamai a ofisoshin jam'iyyar APC da PDP a Kano

Hukumar 'yan sanda ta cafke makamai a ofisoshin jam'iyyar APC da PDP a Kano

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu muggan makamai a ofisoshin jam'iyyar APC da kuma na PDP da ke karkashin karamar hukumar Tudun Wada kamar yadda rahotanni suka ruwaito.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sandan ta kuma samu nasarar cafke 'yan bangar siyasa takwas masu alaka da wannan muggan makamai kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar ya bayyana, DSP Haruna Abdullahi.

Kwamishinan 'yan sandan Kano; CP Muhammad Wakil

Kwamishinan 'yan sandan Kano; CP Muhammad Wakil
Source: UGC

Da ya ke bayar da tabbacin sa a kan wannan lamari, DSP Abdullahi ya ce muggan makamai da suka shiga hannu sun hadar da adduna, wukake, miyagun kwayoyi da kuma sauran muggan makamai masu barazana ga lafiya.

Yayin tuntubar shugaban jam'yyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas, ya shaidawa manema labarai cewa ba bu dan jam'iyyar APC ko guda da ya shiga hannun jami'an tsaro a sanadiyar alakar sa da makaman da ta kai hannu gare su.

Cikin zayyana nasa jawabin, sakataren jam'iyyar PDP na jihar Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya ce hukumar 'yan sanda ta bayar da belin 'ya'yan jam'iyyar su bayan da ta gaza kama su da zargin da ta ke tuhumar su.

KARANTA KUMA: An cafke 'yar Najeriya da hodar Iblis a birnin Sin

Kazalika kwamshinan 'yan sandan jihar CP Muhammad Wakil ya bayyana cewa, ya na nan daram kan bakin aikin sa kuma an daina jin duriyar sa a halin yanzu sakamakon shudewar kakar zabe kamar yadda ya bayyana manema labarai na BBC Hausa a makon da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel