Tsohon shugaban kasar Kenya ya rasa dansa na farko

Tsohon shugaban kasar Kenya ya rasa dansa na farko

-Idan ajali yayi kira, babban dan Arop Moi ya rasu

-Kenya na cikin juyayin mutuwar da a wajen tsohon shugaban kasar, Arap Moi

Jonathan Moi da a wajen tsohon shugaban kasar Kenya Arap Moi ya mutu. Jonathan din dai ya mutune ranar Juma’a sai dai har yanzu ba’a san dalilin mutuwarsa ba. Jaridar 'The medium' ta bayyana cewa za’a rinka tunawa da wannan mamacin ko dan shahararsa a wajen iya tseren mota.

Iyalan Moi sune suka bada sanarwar wannan mutuwa yayinda wannan abu ya faru kunshe a cikin wata takarda, wacce aka rubutawa “Sanarwar mutuwar Jonathan, a madadin iliahrin iyalan Mzee Moi muna sanar daku cewa Jonathan ya riga mu gidan gaskiya.”

Tsohon shugaban kasar Kenya ya rasa dansa na farko

Marigayi Jonathan Moi
Source: UGC

KU KARANTA:Bayan shekara 18 da aure, wata mata ta haifi yara 5 a jihar Kogi

“Hakika za a rinka tunawa da Jonathan dalilin shahararsa a fannin tseren motoci musamman a wannan lokacin da ake bikin ista. Mutum ne shi mai saukin kai kuma wanda iya hulda da jama’a kwarai da gaske. Wannan mutuwa ta matukar girgizamu, a don haka muna rokon addu’o’inku ga wannan mamacin.

Arap Moi mai shekara 94, ya kasance shugaban kasar Kenya daga shekarar 1978 zuwa 2002. Kafin zamanshi shugaban kasa, yayi zama mataimakin shugaban kasar daga 1967 zuwa 1978.

Moi yanada yara takwas, maza biyar da kuma mata uku. Ga sunayensu kamar haka, Jonathan (Marigayi), Gideon, Philip, Doris Elizabeth Chepkorir, Jennifer, June, Raymond da John Mark.

Mahaifiyarsu mai suna Lena Moi ta kasance matar mahaifin nasu ne tsakanin shekarar 1950 zuwa 1974 kuma ta rasu a shekarar 2004. A shekara 94, Arap Moi shine tsohon shugaban kasar Kenya mafi tsufa dake raye a halin yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel