Aisha zata bude jami’ar Muhammadu Buhari

Aisha zata bude jami’ar Muhammadu Buhari

-Sabuwar jami'a mai sunan Shugaba Buhari na nan tafe, shin ko a ina za'a bude wannan jami'a?

-Kasancewar ilimi nada matukar amfani, Aisha zata bude jami'ar hadin gwiwa mai suna "Jami'ar Muhammadu Buhari"

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana kudurinta na bude jami’a mai zaman kanta wacce zata sanyama suna “Jami’ar Muhammadu Buhari”. Tayi wannan furucin ne ranar Assabar wurin wani taro da ta hada a Yola tare da masu kishin garin na Adamawa.

Aisha, wacce bata fadi lokaci ko wurin da wannan jami’ar zata kasance ba, tace za’a bude wannan jami’ane ta hanyar hadaka da kasashen Sudan da Qatar. Da take zayyana matsalolin dake fuskantar ilimi a jihar da ma sauran sassa daban-daban na jihar, Aisha tayi kira ga yan asalin wannan jiha ta Adamawa da suyi iya bakin kokarinsu domin marawa gwamnati baya wajen shawo kan matsalar.

Aisha zata bude jami’ar Muhammadu Buhari

Aisha Buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Bayan shekara 18 da aure, wata mata ta haifi yara 5 a jihar Kogi

“Ba zan iya cewa ga abinda zamuyi ba na tilas domin bada taimakonmu ga kokarin da gwamnati keyi ba, sai dai kawai zan iya bada shawarwari akan irin ababen da idan mukayi zasu taimaka kwarai da gaske.

“A daidai wannan gaba, zan so a bude wani asusu na musamman a jihar Adamawa wanda zai kasance ya ta’allakane fannin ababen kawo cigaba a fadin jihar nan, ta yanda za’ayi amfani da kudin kana kuwa a kaddamar da ayukan.”

Ambasada Fati Ballah ita kuwa kira tayi ga al’ummar jihar, da su kasance masu hakuri da juna sa’anan kuma ta bada shawarar cewa yakamata a kafa kwamiti wanda zai kawo tsare-tsaren da za’a bi domin ciyar da jihar tasu gaba.

Manya-manyan mutane da dama sun halarci wannan taro daga cikinsu akwai; Alhaji Sadiq Daware, Farfesa Shehu Iya, Farfesa Auwal Abubakar, Mrs Hellen Mathias, Mallam Umar Abubakar, Janar Buba Marwa da wasu jiga-jigan jam’iyun APC, PDP da ADC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel