Kotun hukumar kiyaye hadurra (FRSC) ta Kano ta gurfanar da mutum 32 a gabanta lokacin bikin ista

Kotun hukumar kiyaye hadurra (FRSC) ta Kano ta gurfanar da mutum 32 a gabanta lokacin bikin ista

-Hukumar kiyaye hadurra ta shirya tsaf domin gudanar da bikin ista lami lafiya

-Ko dai ka bi dokokin hanya, ko kuma hukumar kiyaye hadurra ta kai ka kotu

Wata kotu wacce ke karkashin hukumar kiyaye hadurra ta kasa dake Kano ta gurfanar da mutum 32 a gabanta bisa laifin saba dokar hanya daban-daban. Jami’in hulda da jama’a na hukumar mai suna, Kabiru Daura shine ya bada wannan sanarwar ranar Assabar a Kano.

Daura yace, mutunae 38 ne aka kama sannan aka kai su gaban kotun ranar Alhamis yayinda kotun ta sallami mutum 6 daga cikinsu. Ya bayyana mana cewa, jami’an hukumar 853 aka baiwa umurnin kula da hanyoyi domin bukukuwan ista.

Kotun hukumar kiyaye hadurra (FRSC) ta Kano ta gurfanar da mutum 32 a gabanta lokacin bikin ista

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Bayan shekara 18 da aure, wata mata ta haifi yara 5 a jihar Kogi

Har wa yau, akwai motoci na sintiri guda 14, motar dake kai mutum asibiti guda biyu da kuma babbar mota guda daya domin janye abubuwan da kan iya tare hanya wacce ke aiki na tsawon awa 24.

A cewarsa, hukumar tasu ta shirya hanyar wayarwa mutane da kai, musamman a wuraren ibada da kuma tashoshin mota. Inda yace makasudin yin hakan shine domin a kara tunatar da mutane kan abinda suka riga suka sani da ya shafi dokokin hanya.

Haka zalika, ya kara jadaddawa aikin nasu na wannan lokaci zai lura ne da matsalolin da suka shafi daukar mutane ko kaya fiye da kima da kuma rashin amfani da na’uran rage gudu musamman ga masu motocin haya.

Sauran laifukan da zamu duba sun hada da, rashin lasisin tuki, ingancin taya da kuma janye motocin da suka lalace da ma wasu abubuwa na daban daga kan titi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel