Ka rantse da Qur'ani akan ba ka yi magudi a zaben nan ba - Buba Galadima ga Shugaba Buhari

Ka rantse da Qur'ani akan ba ka yi magudi a zaben nan ba - Buba Galadima ga Shugaba Buhari

- Buba Galadima ya bukaci shugaba Buhari da shugabannin jam'iyyar APC da hukumar zabe ta kasa akan su fito su rantse da Qur'ani akan ba su yi magudin zabe ba

- Buba Galadima ya ce ya na da tabbacin cewa jam'iyyar PDP ce ta lashe zaben shugaban kasa sai aka yi magudi aka ba wa Buhari

Tsohon abokin Buhari, kuma babban dan adawan gwamnatin shugaba Buhari, Buba Galadima, ya kalubalanci shugaba Buhari akan ya yi rantsuwa da Qur'ani akan cewar bai yi magudi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Fabrairun wannan shekarar.

Galadima, wanda ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, ne ya lashe zaben shugaban kasa, sai jam'iyyar APC da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa suka yi magudi suka ba wa shugaba Buhari.

Ka rantse da Qur'ani akan ba ka yi magudi a zaben nan ba - Buba Galadima ga Shugaba Buhari

Ka rantse da Qur'ani akan ba ka yi magudi a zaben nan ba - Buba Galadima ga Shugaba Buhari
Source: Facebook

Ya bayyana zaben a matsayin abin kunya yayin da ya kalubalanci shugaban kasa da shugabannin APC su rantse da littafi masi tsarki akan cewar Buhari ne ya lashe zaben.

"Wannan zaben abin kunya ne ga gwamnatin Najeriya, saboda kowa ya san cewa hukumar zabe da hukumomin tsaro na kasar nan su ne suka hada baki da jam'iyyar APC suka yi magudin zaben nan," in ji Galadima.

KU KARANTA: Jerin jihohin da suka shirya biyan albashin naira 30,000

"Na kalubalanci Buhari da shugabannin APC da su yi rantsuwa da Alkur'ani mai girma, da kuma Bible idan sun tabbata cewa Buhari ya lashe zaben. Idan har suna da tabbacin cewa Buhari ne ya lashe zaben, daga kan Buhari har shugabannin APC ban bar kowa ba na kalubalance su akan su rantse."

Galadima ya kara da cewa tsarin gudanar da zaben nan ya nuna cewa Buhari ba yaki yake da cin hanci da rashawa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel