An bukaci dukkanin 'yan siyasar jihar Kano su bayyana kadarorinsu kafin wa'adinsu ya kare

An bukaci dukkanin 'yan siyasar jihar Kano su bayyana kadarorinsu kafin wa'adinsu ya kare

- Wata cibiya ta bukaci dukkanin 'yan siyasar jihar Kano da za su bar Ofis da su fara bayyana kadarorinsu kafin lokacin barin ofis na sun ya yi

- Cibiyar ta ce bijirewa umarnin ta zai sanya fushin hukuma ya mutum

Cibiyar ladabtar da ma'aikata ta jihar Kano ta na tunatar da duk masu mukami dake jihar da su tabbatar da sun bayyana kadarorinsu kafin su bar ofis.

Sanarwar da cibiyar ta fitar wacce daraktan cibiyar, Umar Saulawa ya sanyawa hannu, sannan kuma ya sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya da ke Kano a yau Asabar dinnan.

An bukaci dukkanin 'yan siyasar jihar Kano su bayyana kadarorinsu kafin wa'adinsu ya kare

An bukaci dukkanin 'yan siyasar jihar Kano su bayyana kadarorinsu kafin wa'adinsu ya kare
Source: Twitter

Ya ce akwai bukatar masu mukamai na jihar da su bayyana kadarorinsu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada.

"Muna tunatar da duk wadanda su ke da mukamai a jihar nan da su zo su bayyana kadarorinsu a ofishin mu kafin wa'adin mulkin su ya cika," in ji shi.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya ba da wasu dalilai da ya sa Najeriya ba za ta taba gyaruwa ba

Ya ce rashin bin umarnin cibiyar zai iya zama matsala kuma ya sa doka ta hau duk wanda bai yi biyayya ga umarnin cibiyar ba.

Kwanan nan ne dai aka sake gabatar da zabe kashi na biyu a jihar Kano, yayin da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC wato gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya lashe zabe, inda ya kayar da dan takarar jam'iyyar PDP Abba K. Yusuf. Hakan ya bashi damar hayewa kujerar gwamnan jihar a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel