Harin Sojoji bai kaiwa garemu, muna samun labarin zuwansu tun kan su zo - Yan bindigan Zamfara

Harin Sojoji bai kaiwa garemu, muna samun labarin zuwansu tun kan su zo - Yan bindigan Zamfara

Yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara sun bayyana cewa suna samun labarin dukkan wani motsi da jami'an Sojoji ke yi na yunkurin kawo musu hari.

Wannan ya bayyana ne a wani faifan rediyo tsakanin daya daga cikin yan barandan da wani sarkin gargajiya a jihar Zamfara, jaridar Punch ta samu rahoto.

Ga yadda tattaunansu ya kasance:

Dan bindiga: "Allah ya riga ya ba ka kujeran da idan kayi magana, mutane zasu ji. Wannan rikicin ya addabi jiharmu tsawon shekaru shida kenan."

"Sun kashe mutane na; sun kashe yan uwana; sun kashe mata na da yara na. Sun kashe dabbobi na. Sai na shiga harkar yan bindigan tunda an kashe min kowa. Amma yanzu na dawo gida, shin za ku karbe ni a matsayin dan gari?"

Sarki: "Haka ne"

Dan bindiga: "Ka kira dukkanin fadawanka da mutanen gari. Ka basu shawaran duk inda suka ganmu, su hada kai da kungiyar Miyyeti Allah. Za'a samu zaman lafiya."

"Idan akayi hakan, za'a samu zaman lafiya. Amma idan kuka ce yan sanda da Soji za'a kawo Zamfara, hakan ba zai kawo lafiya ba. Za'a cigaba da zub da jini ne."

Sarki: "Haka ne"

Dan bindiga: "Wani zubin za ka samu labarin cewa an kai hari inda yan bindiga suke, amma gobe sai mu sake kai hari a kusa da wajen. Dalilin da yasa bama-baman soji ba zai yi aiki ba shine kafin jirginsu ya iso, mun samu labari."

Sarki: "Ba mu goyon bayan hare-haren bama-baman"

Dan bindiga: "Kafin jirginsu ya tashi daga bariki, mun samu labari. Kuma idan suka kai harin, tsuntsaye da dabbobi kawai suke kashewa. Idan kuma aka tura sojin kasa su kawo mana hari, tun kan su iso zamu samu labari. Muna son ka hana yan banga fitowa ga baki daya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel