Abinda yasa ruwan wutar dakarun sojin sama ba zai kashe mu ba - 'Yan bindiga Zamfara

Abinda yasa ruwan wutar dakarun sojin sama ba zai kashe mu ba - 'Yan bindiga Zamfara

- 'Yan bindigar da ke kisan jama'a a jihar Zamfara sun ce luguden wuta da dakarun sojin sama ke yi ba zai kashe su ba

- A wata hira da daya daga cikin 'yan bindgar ya yi da wani sarki a Zamfara, ya ce su na samun bayanan sirri a kan harin dakarun soji

- 'Yan bindigar sun ce za a cigaba da samun zubar da jini a jihar Zamfara matukar gwamnati ta cigaba da aika rundunar jami'an tsaro

Duk da irin kokarin da rundunar soji da ragowar jami'an tsaro ke yi wajen kawo karshen aiyukan ta'addanci a Zamfara, 'yan bindigar da suka addabi jihar sun bayyana cewar luguden wutar da dakarun sojin sama (NAF) ke yi ba zai kashe su ba, saboda su na samun bayanan sirri kafin a kai hari a maboyar su.

Jaridar Sahara Reporters ta rawaito cewar, daya daga cikin 'yan bindigar ne ya bayyana hakan ga wani sarki a Zamfara, a cikin wani faifan sautin murya da jaridar Punch ta samu.

A cikin faifan sautin, dan bindigar, da ba a san ko waye ba, ya ce za a cigaba da samun zubar da jini a jihar Zamfara matukar gwamnati ta cigaba da aika rundunar jami'an tsaro.

Abinda yasa ruwan wutar dakarun sojin sama ba zai kashe mu ba - 'Yan bindiga Zamfara

Jiragen yakin dakarun sojin sama
Source: Facebook

A wani bangare na faifan sautin, dan bindigar ya ce: "wasu lokutan za a ji labarin dakarun soji sun yi ruwan wuta a maboyar 'yan bindiga, amma washegari sai a ji labarin 'yan bindigar sun kara kai hari wani kauye da ke kusa da wurin da sojojin suka kai hari."

Sai sarkin ya amsa masa da cewar: "mu ma mu na goyon bayan ruwan wutar da dakarun sojin ke yi."

DUBA WANNAN: Har ila yau: 'Yan bindiga sun yiwa mutane 16 kisan wulakanci a kauyen Zamfara

Sai dan bindigar ya cigaba da cewa: "ba zasu samu damar kashe mu ba, saboda tun kafin jirginsu na yaki ya tashi daga sansaninsu, za mu samu labarin tashinsa da wurin da zai kai hari. A saboda haka kafin su zo mun canja wuri, sai dai su kashe dabbobi da tsuntsayen da ke wurin.

"Hatta sojojin kasa ba zasu samu damar kashe mu ba, don kafin su zo tuni labari ya iske mu. Allah ne yake taimakon mu."

Kazalika, dan bindigar ya shaida wa sarkin cewar ba za a samu saukin zubar da jini a jihar Zamfara ba matukar gwamnati za ta cigaba da aika rundunar sojoji da sauran jami'an tsaro domin su murkushe su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel