Kuma dai: 'Yan bindiga sun kara kashe mutane 16 a Zamfara

Kuma dai: 'Yan bindiga sun kara kashe mutane 16 a Zamfara

'Yan bindiga sun kashe a kalla mutane 16 a wani sabon hari da suka kai ranar Alhamis a kauyen Marke da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa a daya daga cikin labaranta na ranar Asabar.

Mazauna kauyen sun ce 'yan bindigar sun isa garin a kan babura, sannan sun bude wuta a kan jama'a. Sun debi shanu da ragowar kayan amfani da dabbobi kafin su gudu zuwa maboyar su a cikin daji.

Wani mazaunin garin da ya yi magana da wakilin jaridar Daily Trust ya ce 'yan bindigar sun datse kawunan wasu mutanen, yayin da suka farke cikin wasu da wuka, suka cire musu wasu kayan ciki.

Kuma dai: 'Yan bindiga sun kara kashe mutane 16 a Zamfara

Jama'a a layin karbar asirin tsare kai a wata kasuwa a Zamfara
Source: Twitter

"Yanzu haka da nake magana da ku, mu na makabarta domin binne mutanen da aka kashe. Na tabbatar da mutuwar mutane 16. Dukkan mutanen kauyenmu sun shiga cikin halin alhini da dimuwa," a cewar mutumin.

DUBA WANNAN: Kisan fararen hula: Rundunar sojin sama ta mayar wa sarakunan Zamfara

Jaridar ta ce ba ta samu damar jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ba kafin ta wallafa rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel