Majalisa: Matasan Arewa sun ce allan fur ba su yadda da Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa ba

Majalisa: Matasan Arewa sun ce allan fur ba su yadda da Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa ba

Bayan shugabannin jam'iyyar APC mai mulkisun nuna zabin su na kakakin majalisar wakilai ta tarayya, sai gashi kungiyar matasan arewa ta kekasa kasa ta ce allan fur ba za ta yadda da wannan zabi na jam'iyya ba, inda ta bukaci jam'iyyar ta kyale 'yan majalisu su zabi shugabannin su da kansu

Kungiyar Matasan Arewa (AYAF) ta yi watsi da zabin jam'iyyar APC mai mulki na tsayar da Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai na tarayya.

Sanarwar da kungiyar ta fitar, wacce shugaban kungiyar Mohammed Sani Kabir, mataimakinshi Salisu Abdulrahman da sakataren kungiyar Ben Alege, suka sanyawa hannu, sunce yarjejeniyar ta sabawa yankin arewa a zaben shugaban kasa da za ayi na shekarar 2023.

Kungiyar ta ce ta na goyon bayan 'yan majalisar wakilai, wadanda suka nuna rashin goyon bayansu ga zabin da jam'iyyar ta yi, kungiyar ta ce zabin da jam'iyyar APC ta yi ba zai amfanawa yankin arewa da komai ba.

Majalisa: Matasan Arewa sun ce allan fur ba su yadda da Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa ba

Majalisa: Matasan Arewa sun ce allan fur ba su yadda da Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa ba
Source: Twitter

Kungiyar ta bukaci shugabannin jam'iyyar APC da su kyale 'yan majalisu su zabi wanda zai shugabance su, sannan kuma ta bukaci 'yan majalisu da su lura dakyau wurin zabar shugaba wanda zai kawo cigaba ga kasar nan.

"Muna kira ga 'yan majalisar wakilai na arewa da su tsaya tsayin daka, kuma kada su bari shugabannin jam'iyya sun canja musu ra'ayi akan ra'ayin mutanen yankin arewa," in ji kungiyar.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya ba da wasu dalilai da ya sa Najeriya ba za ta taba gyaruwa ba

Har ila yau, kungiyar ta gargadi shugabannin jam'iyyar APC akan yadda suka yi watsi da kundin tsarin mulkin Najeriya ta hanyar tilasta tsayar da wasu 'yan majalisu ba bisa ga yadda dokar kasa ta tsara ba, sannan kungiyar ta yi kira ga jam'iyyar ta kyale 'yan majalisu su zabi wanda suke so ya shugabance su, ba wai dole sai Tinubu da Oshiomhole sun tilastawa mutane Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila a majalisa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel