Karin albashi zai iya jawo rikici a Najeriya - Wani jigo a jam'iyyar APC

Karin albashi zai iya jawo rikici a Najeriya - Wani jigo a jam'iyyar APC

Wani jigo a jam'iyyar APC ya ce karin albashi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kai ranar Alhamis dinnan da ta gabata zai iya barin baya da kura, domin kuwa karin albashin zai iya kawo rikici da a kasar nan

Tsohon ministan watsa labarai, kuma jigo a jam'iyyar APC, Prince Tony Momoh, ya yi gargadin cewa sabon karin albashi da aka yi na N30,000, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu domin ya zama dokar kasa a ranar 18 ga watan Afrilu, na iya haifar da rikici a kasar nan.

A cewar Momoh wanda ya yi jawabi a Abuja a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, lokacin da ake bikin murnar cikar shi shekaru 80 a duniya, da kuma murnar cikar shi shekaru 50 da yin aure a jiya 19 ga watan Afrilun nan, ya ce bai ga amfanin murna da mutane ke yi ba, tunda da yawa daga cikin gwamnoni ana binsu bashin albashin N18,000, saboda haka bai tunanin wanda ake binshi bashin N18,000 zai iya biyan N30,000 ba.

Karin albashi zai iya jawo rikici a Najeriya - Wani jigo a jam'iyyar APC

Karin albashi zai iya jawo rikici a Najeriya - Wani jigo a jam'iyyar APC
Source: Facebook

"A nawa hasashen karin albashin nan zai iya haifar da rikici a kasar nan saboda da yawa daga cikin gwamnonin da su ke biyan N7,500 kafin a mai da shi N18,000 har yanzu ba su iya biyan N18,000. Kuma sun riga sun fada cewar baza su iya biya ba. Kuma hakan zai iya jawowa ma'aikata su tafi yajin aiki. Da hakan ta faru kuma shikenan kasar nan ta shiga cikin matsala.

KU KARANTA: Jerin jihohin da suka shirya biyan albashin naira 30,000

"Albashin N30,000 ba wai albashin da mutum zai ta faman ci bane har karshen rayuwarshi. Mene ne yawan ma'aikatan Najeriya da ke da damar samun albashin N30,000? Menene yawan ma'aikatan gwamnati idan aka kwatanta da yawan mutanen Najeriya?" In ji Momoh.

A ranar Alhamis dinnan ne da ta gabata dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar karawa ma'aikata albashi a kasar nan daga N18,000 zuwa N30,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel