Jami’o'i 7 sun samu sabbin cibiyoyin bincike mai zurfi

Jami’o'i 7 sun samu sabbin cibiyoyin bincike mai zurfi

-Jami'ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato itace jami'a cikon ta bakwai da samun wannan cibiya ta yin bincike mai zurfi

-Bunkasar ilimin jami'a bai samuwa sai da yin bincike mai zurfi

A bisa ga yinkurin samar da ilimin kimiyyar adana kudade, babbar kungiyar masu kula da adana kudade ta kasa wato ‘ANAN’ ta baiwa jami’o’i bakwai cibiyoyin bincike mai zurfi. Jagoran wannan kungiyar na kasa mai suna Alhaji Shehu Ladan ne ya bada sanarwar a Sakkwato.

Shugaban yace wannan cibiyar wacce kudinta ya kama kimanin naira miliyan dari, da aka bude a Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato itace ta bakwai. Kuma karkashin kulawar kungiyar tasu ne wadannan cibiyoyin suke.

Jami’o'i 7 sun samu sabbin cibiyoyin bincike mai zurfi

Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto
Source: UGC

KU KARANTA:APC: Sabon karancin albashin N30,000 dayane daga cikin alkawuranmu da muka cika

Sauran jami’o’i shidan da keda wannan cibiyar sun hada da; Jami’ar jihar Nasarawa, Jami’ar jihar Kogi, Jami’ar Jos, Jami’ar gwamnatin tarayya ta harkokin noma dake Abeokuta, Jami’ar Ahmadu Bello da Jami’ar Nnmadi Azikwe.

Ladan, yayinda yake jawabi a wajen taron bude wannan cibiya, yace kungiyarsu itace tayi wannan gini tare da sanya duk abubuwan da ake bukata domin cigaba da gudanar da aiki a wannan cibiya.

Da yake jawabin godiya, shugaban jami’ar Danfodiyo, Farfesa Abdullahi Zuru cewa yayi jami’ar tayi matukar murna da wannan cigaba da kungiyar ta kawo mata, inda ya kara da cewa zasuyi amfani da wannan cibiya domin bunkasa bincike mai zurfi wanda zai kawowa al’umma cigaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel